’Yan bindiga sun kashe manoma akalla 27 a wani sabon hari a unguwar Bindi-Jebbu da ke yankin Tahoss da ke Karamar Hukumar Riyom da ke Jihar Filato.
Maharan sun jikkata wasu da dama a yayin da aka garzaya da mamanan da kuma wadanda suka jikkata zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos domin ba su kulawa.
Aminiya ta samu labarin cewa waɗanda harin ya rutsa da su sun hada da ƙananna yara da manya maza da mata.