✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya faru tsakani na da DSS bayan kama ni — Ɗan Bello

Sai dai Ɗan Bello ya ce bai yi mamakin kama shi da aka yi ba, domin a Najeriya komai zai iya faruwa.

Wasu da ake zargin Jami’an Hukumar Farin Kaya (DSS), sun kama fitaccen mai barkwancin nan a kafafen sada zumunta, Bello Habib Galadanci, wanda aka fi sani da Ɗan Bello, a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano.

Sun kama shi ne bayan isowarsa filin jirgin saman, wanda hakan ya jawo hankalin mutane da dama, ciki har da fasinjoji da ma’aikatan filin jirgin.

Sai dai Ɗan Bello cikin wata hira ta wayar tarho da ya yi da kafar DCL, ya bayyana abin da ya faru, inda ya ce: “Dana sauko wasu mutane wanda kana ganinsu ka san hukumomi ne suka karɓi fasfo da sauran kayayyakina.

“Sai suka ga mota ne na hau mu tafi, ana haka ne sai ga barista Abba Hikima nan, ya zo sai aka yi doguwar magana cikin turanci”, in ji shi.

Ya ƙara da cewa: “Bayan kamar awa ɗaya da rabi sai suka shi kenan za mu iya tafiya. Wannan shi ne abin da ya faru.”

Wasu da lamarin ya faru a idonsu, sun ce suna tunanin jami’an sun zo ne daga Abuja, kuma sun kama Ɗan Bello ba tare da bayyana dalilinsu ba, wanda hakan ya sa mutane da dama cikin ruɗani.

Amma wata majiya ta tabbatar wa Aminiya cewa jami’an sun sako shi bayan ’yan mintuna kaɗan da kama shi.

“Lallai DSS ne suka kama shi, amma sun sake shi daga baya. Wataƙila sun samu sabon umarni ne don a sake shi. Yanzu yana cikin ƙoshin lafiya,” in ji majiyar.

Sai dai Ɗan Bello, ya ce bai yi mamakin kama shi da aka yi bayan isowarsa Najeriya.

“A Najeriya muke. Har da kayan gidan yarina na taho a shirye.

“Ina son mutane su kwantar da hankalinsu, ina lafiya sannan Allah Ya ƙara mana kwanciyar hankali mu saita ƙasarmu, mu ɗora ta a kan hanya wanda ba su fahimci inda aka dosa ba, su fahimta insha’Allah,” a cewar Ɗan Bello.

Ɗan Bello dai, ya yi fice a Arewacin Najeriya, inda yake wallafa bidiyoyinsa na barkwanci da suka kan taɓo batutuwan siyasa da zamantakewa.

Mutane da dama na kallon abubuwan da yake wallafawa a Intanet, inda yake haɗa barkwanci da tsokaci kan abubuwan da ke faruwa a ƙasar nan.

Zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, hukumomi ba su bayyana dalilin kama shi ba, kuma DSS ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba.