Hukumar Tsaro ta DSS ta saki matashin nan mai barkwanci, Bello Habib Galadanci, jim kaɗan bayan sun kama shi a Jihar Kano.
Jami’an DSS sun kama Dan Bello ne a Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano kuma wasu majiyoyi na zargin daga Abuja jami’an suke.
Aminiya ta gano saukar matashin da ke zaune a ƙasar China a Najeriya ke da wuya jami’an DSS suka yi awon gaba da shi.
Sai dai kuma rahotanni da muka samu daga bisani sun nuna cewa jami’an tsaron sun sake shi, bayan ya yi ’yan mintoci a hannunsu.
Bayan nan ne Ɗan Bello ya wallafa hotonsa da tare da matashin lauya ɗan gwagwarmaya, Abba Hikima a cikin mota.
A ƙarƙashin hoton da ya wallafa a shafinsa na Facebook, kuma ya rubuta, “Masha Allah, kowa ya bar gida.”
Kawo yanzu dai babu bayani daga hukumomin tsaro ko Ɗan Bello game da dalilin tsarewar da aka yi masa da kuma abin da ya wakana tsakaninsu.
Ɗan Bello dai ya yi ƙaurin suna wajen yin bidiyon barkwanci kan matsalolin shugabanci da cin hanci a Najeriya.
A baya-bayan nan sakonni da ya wallafa kan matsalar fanshon ’yan sanda da ta matsalar albashin malaman jami’a sun ɗauki hankali matuƙa.