✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun gurfanar da mutum 29 a kotu kan zargin kashe DPO a Kano – ’Yan sanda

Rundunar ’Yan Sanda ta jihar Kano ta ce ta gurfanar da mutum 29 da ta kama bisa zarginsu da hannu a kashe DPO na garin…

Rundunar ’Yan Sanda ta jihar Kano ta ce ta gurfanar da mutum 29 da ta kama bisa zarginsu da hannu a kashe DPO na garin Rano da ke jihar, CSP Baba Ali da sauran laifuffuka.

Kakakin rundunar a jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Alhamis, inda ya ce an gurfanar da su ne a gaban kotun majistare mai lamba 20 da ke Nomansland a Kano.

Gurfanarwar dai ta biyo bayan kammala bincike kan kisan wanda ya ja hankalin mutane a ciki da wajen jihar.

Kiyawa ya ce 14 daga cikin mutanen, da suka hada da Bala Yusuf, Bala Mohammed, Abdulrashid Ibrahim, Abdullahi Salisu Kere, Sadiq Buhari, Yunusa Adamu, Musa Minkaila, Mamuda Mohammed, Ismail Mamuda, Usman Shu’aibu, Musa Hassan Black, Abdulrashid Munkail, Umar Ado Nadada da Sabitu Abubakar, dukkansu ’yan asalin karamar hukumar ta Ranon ne, kuma ana zarginsu da aikata kisan kai da sauran laifuffuka.

Sauran laifuffukan da ake zargin nasu da su sun hada da hadin baki, tayar da zaune tsaye, kone-kone, ketare iyaka, jikkatawa da kuma sata.

Ragowar mutum 15 din kuma wadanda su ma aka dauki bayansu a lokacin bincike ana zarginsu da hadin baki da tayar da zaune tsaye da kuma iza wutar rikici kan kisan DPOn da kuma lalata gini.

Rahotanni dai sun bayyana yadda aka kasha marigayi CSP Baba Ali a Rano, bayan mutanen gari sun zarge shi da hannu a kashe wani wanda aka tsare a ofishin ’yan sanda.

“Rundunarmu tana ba mutane tabbacin cewa za a yi adalci a wannan shari’ar, sannan tana godiya kan sakonnin ta’aziyya da addu’o’i da taimako da kuma fahimta da hadin kan da mutane suka bayar a lokacin da ake binciken,” in ji sanarwar.

Kiyawa ya kuma ce duk da an fara shari’ar wadanda suka zo hannu, rundunar ta sha alwashin gani ta ci gaba da farautar duk ragowar masu hannu a cikin aika-aikar domin ganin su ma sun girbi abin da suka shuka.