Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Italiya, FIGC, ta sanar da jingine wasannin gasar Serie A, B, da C, saboda alhinin rasuwar shugaban ɗarikar Katolika, Fafaroma Francis.
Shugaban hukumar FIGC, Gabriel Gravina ya ce, “Harkar ƙwallon ƙafa ta Italiya tana taya jimami ga miliyoyin al’umma kan rasuwar Mai Alfarma Fafaroma Francis.
Ƙungiyoyin da dakatarwar ta shafa sun haɗa da Juventus, Lazio, Parma Calcio, Cagliari, Fiorentina, Genoa, Torino, Udinese.
A safiyar Litinin 21 ga Afrilu ne Fadar Cocin Katolika da ke Vatican City ta sanar da rasuwar Fafaroma Francis mai shekaru 88, wanda ke shugabantar Cocin, kuma shugaban birnin Vatican City.
Miliyoyin mutane a Italiya da kuma faɗin duniya sun shiga alhini saboda rasuwar malamin adinin.
Wannan ya sa aka ɗauki matakin jingine duka lamuran wasanni don nuna girmamawa ga rasuwar.
An soke duka wasannin da aka shirya bugawa ranar Litinin ta Easter, inda a babbar gasar Serie A ta Italiya, Juventus za ta kara da Parma, Lazio da Genoa, Torino da Udinese, Cagliari da Fiorentina.
Haka ma a ƙananan gasannin Italiya na Serie B da Serie C su ma an soke buga wasannin da aka tsara a baya.
Hukumar ta FIGC ta fitar da sabon jadawali da ke nuna cewa za a buga wasannin a ranar 23 ga wannan watan.
A halin yanzu dai galibi ƙungiyoyin suna da sauran wasanni biyar ne kafin kammala kakar gasanni ta bana.
Tarihi ya nuna cewa ko a 2005 da Fafaroma John Paul II ya rasu, an ɗauki irin wannan mataki.