Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars da gidan rediyon Faransa RFI Hausa suka sanya hannu kan yarjejeniya ta Naira Miliyan 100.
A karkashin yarjejeniyar da aka kulla a yau alhamis, kungiyar za ta karbi tsabar kudi Naira miliyan 45m da kuma samar da rigunan kakar wasa ga dukkan ‘yan wasan.
Haka kuma RFI za ta horar da jami’an yada labaran kulob din tare da wallafa wasu labarai da suka shafi kungiyar.
- Sojoji sun kashe wasu ’yan bindiga a Filato
- Rashin wajen sauka a filin jirgin Katsina ne ya hana ni zuwa jana’izar Buhari – Akpabio
Sabon Manajan Pillars Ahmed Musa da Sakataren kungiyar ne suka sanya hannu a takardar a madadin kungiyar, yayin da Shugaban Sashen Hausa na RFI Joseph Penney da Babban Editan Bashir Ibrahim Idris suka sanya hannu a madadin kungiyar.
“Wannan ne karon farko da RFI ta dauki nauyin daukar nauyin wani abu da ya shafi wasan kwallon kafa a tarihi.” inji Penney
Yarjejeniyar ta tsawon shekara guda ce kawai.