✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ma’aikatun da Tinubu ya rushe sun samu N2.4tr a Kasafin 2025

Kowacce daga cikin rusassun ma'aikatun biyu an ware mata kuɗaɗen manyan ayyuka da albashi da kuma na ayyukan gudanarwa

Shugaban Kasa Bola Tinubu ya ware Naira tiriliyan 2.3 a matsayin kasafin shekarar 2025 ga Ma’aikatar Wasanni da Ma’aikatar Cigaban Neja da dangoginta waɗanda ya riga ya rushe su.

A watan Oktoba bayan taron Majalisar Zartaswa ta Ƙasa, wanda Shugaba Tinubu ya jagoranta, Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya sanar da rushe ma’aikatar Wasanni da ta yankin Neja Delta.

Sauran su ne ma’aikatun kula da cigaban Arewa maso Gabas da ta Arewa maso Yamma da ta Kudu maso Yamma da ta Kudu maso Gabas.

Ministan ya bayyana cewa ayyukan Ma’aikatar Wasanni za su koma ƙarƙashin Hukumar Wasanni ta Ƙasa a yayin da ayyukan Ma’aikatar Neja Delta da dangoginta kuma za su koma ƙarƙashin sabuwar Ma’aikatar Kula da Cigaban Yankuna.

Ya ƙara da cewa Ma’aikatar Cigaban Yankuna ita ce za ta haɗe ayyukan rusassun ma’aikatun kula da Neja Delta da ta yankin Arewa maso Gabas da ta Arewa maso Yamma da Kudu maso Yamma da kuma Kudu maso Gabas.

Aminiya ta bibiyi kasafin 2025 na Naira tiriliyan 49.7 da Shugaba Tinubu ya gabatar wa Majalisar Dokoki ta Ƙasa, inda wakilanmu suka gano cewa kowacce daga cikin rusassun ma’aikatun an ware mata kuɗaɗen gudanarwa da na albashin ma’aikata da kuɗaɗen manyan ayyuka.

An jimillar Naira tiriliyan 2.4 ga rusasshiyar Ma’aikatar Neja Delta da dangoginta — Naira tiriliyan 2.205 na albashi da Naira biliyan 24.5 na manyan ayyuka sai Naira biliyan 1.7 na gudanarwa.

Rusasshiyar Ma’aikatar Wasanni kuma an ware mata jimillar Naira biliyan 95, da suka haɗa da Naira biliyan 79.9 na manyan ayyuka da Naira biliyan 14 na gudanarwa, sai albashi Naira miliyan 900.

Sai dai kuma wakilanmu sun lura cewa ba a ware ko sule ba a kasafin na 2025 ba ga sabuwar Ma’aikatar Kula da Cigaban Yankuna da Hukumar Wasannin. Hasali ma babu sunayensu a kasafin.

Ya zuwa yanzu ba za iya cewa ko kuɗaɗen da aka ware wa rusasshiyar Ma’aikatar Neja Delta dangoginta ne za a kai wa sabuwar ma’aikatar kula da yankunan ba, ko ma ma’aikatar wasanni za a ba wa Hukumar Wasanni.

Amma masana sun bayyana cewa idan ma kuɗaɗen da aka ware wa rusasshiyar Ma’aikatun Neja Delta da Dangoginta za a ba wa sabuwar ma’aikatar kula da cigaban yankuna, wannan ya nuna ƙarara cewa ba a yi aiki yadda ya kamata ba wajen tsara kasafin na 2025.

Wasu abubuwa da suka ɗauki hankali a kasafin sun hadvafa kuɗaɗen da aka ware a kasafin domin kula da Fadar Shugaban Ƙasa, inda aka ware Naira miliyan 125 domin kula da fulawa.

Shugaban ƙasar ya ware Naira miliyan 86 domin kula da dabbobi da kuma Naira miliyan 38.5 na kula da ciyayi da fulawar fadar ta Aso Rock a shekarar.

Kazalika an ware Naira miliyan 165 domin sayen tayoyi masu sulke, baya ga Naira biliyan 4.7 na sayen sababbin motoci.

Kayayyakin motsa jikin Fadar Shugaban Ƙasa za su ci  Naira miliyan 101, a yayin da aka ware Naira miliyan 73 domin sayen na’urorin sadarwa.

Waɗannan na daga cikin abubuwan da aka ware wa Naira biliyan 47 domin kula da Fadar Shugaban Ƙasa a Kasafin na 2025.

Daga ciki akwai kasafin Naira biliyan 5.5 da aka ware domin aikin kwaskwariman fadar, sai gyaran na’urorin laturoni da sauransu da zai ci Naira biliyan shida.

Naira biliyan 1.8 kuma an ware su ne domin ƙarasa aikin gina ofisoshin masu ba da shawara a fadar shugaban ƙasa.

An kuna ware Naira biliyan 12 domin biyan bashin ayyukan gyara da kamfanin Julius Berger ya yi a Fadar Shugaban Ƙasa.

A ranar Laraba ne dai Shugaba Tinubu ya gabatar da kasafin 2025, wanda tuni Majalisar Dattawa ta kammal karatu na biyu a kansa.

A halin yanzu kasafin na gaban kwamitin majalisar domin fara aiki a kansa.