✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hauhawar farashi ya ragu zuwa kashi 23.71 — NBS

Hukumar ta ce an samu sauƙin hauhawar farashi idan aka kwatanta da watan Maris.

Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), ta bayyana cewa hauhawar farashi a Najeriya ya sauka kaɗan a watan Afrilu 2025 zuwa kashi 23.71, daga kashi 24.23 da aka samu a watan Maris.

Wannan na nuna cewa hauhawar farashi ya ragu idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, inda a watan Afrilun 2024 aka samu kashi 33.69.

Wannan ragi da aka samu a watan Afrilu ya kai kusan kashi 10.

Har ila yau, hukumar ta ce hauhawar farashi daga wata zuwa wata ya ragu a watan Afrilu, inda aka samu kashi 1.86, ƙasa da kashi 3.90 da aka samu a watan Maris.

Wannan na nuna cewar hauhawar farashin kaya bai yi tsada da yawa ba a watan Afrilu idan aka kwatanta da watan Maris.

Farashin kayan abinci, wanda yafi shafar rayuwar yau da kullum, ya tsaya a kashi 21.26 a watan Afrilu, idan aka kwatanta da kashi 40.53 a bara.

Wannan ragin ya faru ne sakamakon sauyin yadda ake ƙididdigar bayanai.

A matakin wata-wata, hauhawar farashin kayan abinci ya kasance kashi 2.06 a watan Afrilu, wanda ya ragu daga kashi 2.18 da aka samu a watan Maris.

Ragi farashin wasu kayayyaki kamar garin masara, hatsi, kuɓewa busasshiya, garin doya, wake, da shinkafa ya taimaka wajen samun wannan sauƙi.

A tsaka-tsaki kuwa, hauhawar farashin abinci a cikin shekara guda zuwa watan Afrilu 2025 ya tsaya a kashi 31.43, wanda ya ragu da kashi 1.31 idan aka kwatanta da shekara da ta gabata wanda yake a kashi 32.74.