✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Duk da hauhawar farashi tattalin arzikin Nijeriya ya haɓaka’

Tattalin arzikin ya ƙaru da kashi 4.6 a watanni uku na ƙarshen 2024, i

Bankin Duniya ya sanar da cewa duk da ƙalubalen hauhawar farashin da Nijeriya take fuskanta, tattalin arzikin ƙasar ya ƙaru a shekarar da ta gabata.

Babban bankin ya ce tattalin arzikin Nijeriyar ya samu haɓaka a kusan shekaru goma a 2024, inda a watanni uku na karshen 2024 aka samu haɓaka sosai.

Hakan na ƙunshe cikin wani rahoto da babban jami’in tattalin arzaki na Bankin Duniya a Nijeriya, Alex Sienaert, ya fitar ranar Litinin a Abuja.

Sienaert ya bayyana cewa tattalin arzikin ya ƙaru da kashi 4.6 a watanni uku na ƙarshen 2024, inda ya kuma yi nuni da cewa zai ci gaba da haɓaka a farkon 2025.

Sai dai ya yi gargaɗin cewa hauhawar farashi na ci gaba da zama ƙalubale amma ana sa ran tattalin arzikin Nijeriyar zai haɓaka a wannan shekarar da kashi 3.6.

Nijeriya na ci gaba da fama da hauhawar farashi, inda Sieneart ya yi gargaɗin cewa dole ne a ɗauki matakan tsuke bakin aljihu da tasarrufin kuɗaɗe bisa doka da oda.

Sienaert ya ce harajin gwamnati ya ƙaru da kashi 4.5 sama da na shekarar da ta gabata, wanda “muhimmiyar nasara” ce, da janye tallafi ga kuɗaɗen ƙasashen waje, da kyautata tsarin karɓar haraji da yawan saka kuɗaɗe a asusun gwamnati suka kawo.

Kuɗaɗen shiga masu yawa da aka samu sun taimaka wajen cike giɓin Kasafin Kuɗi da aka yi hasashen ya kai kusan kashi uku a 2024, daga kashi 5.4 da aka samu a 2023.

Manyan matakan da shugaban ƙasar Bola Tinubu ke ɗauka, ciki har da kawo ƙarshen tallafin mai, da janye tallafi kan wutar lantarki da karya darajar naira har sau biyu, sun ƙara matsa lamba ga farashin kayayyaki.