✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan kasuwar da suka ɓoye kayan abinci na tafka asara

A lokacin da farashin ke hauhawa suka sa maƙudan kuɗaɗe suka saya suka ɓoye, da fatan samun gagarumar riba idan buƙatar kayayyakin ta ƙaru a…

’Yan kasuwar kayan abinci sun bayyana yadda suke tafka asara  bayan sun saye wasu kaya sun ajiye suna jiran samun tuna mai tsoka idan kayan sun yi tashin gwauron zabo.

A shekarar bara, ’yan kasuwa, musamman masu hadahadar kayan abinci da na amfanin gona a Nijeriya, kakarsu ta yanke saƙa, saboda tashin gwauron zabon da kayan a ƙasar. Galibin waɗannan amfanin gona na kasuwanci ana fitar da su zuwa ƙasashen a duniya.

Hukumar Bunƙasa Fitar da Kayayyaki ta Nijeriya (NEPC) ta sanar a watan Agusta na shekarar ta 2024, cewa Najeriya ta samu gagarumin ci-gaba a fannin fitar da kayayyaki da ba na man fetur ba a watanni shidan farkon shekarar, inda ta samu kuɗin shiga kimanin dala biliyan 2.7.

Yawan buƙatar kayan a kasuwannin duniya ya kawo hauhawar farashin kayan abinci na yau da kullum da amfanin gona na kasuwanci. An kuma yi hasashen cewa farashin zai ci gaba da tashi a shekarar 2025.

A lokacin da farashin ke hauhawa, ’yan kasuwa da dama sun zuba jari mai yawa, musamman a harkar riɗi da waken suya, da fatan samun gagarumar riba idan buƙatar kayayyakin ta ƙaru a kasuwannin duniya. Sai dai a cikin wani yanayi mai matuƙar ɗaure kai, sai ga shi farashin na ta faɗuwa warwas, musamman a Arewacin ƙasar nan.

Ma’aunin Farashin Kayayyaki (CPI) ya nuna an samu saukar farashin da kimanin kaso 25 cikin 100, daga N87 zuwa N65 a cikin watan Maris din 2025, kamar yadda kamfanin mai zaman kansa na farko a Nijeriya da aka ba lasisin hada-hadar musayar kuɗaɗen kayayyaki, AFEX, ya bayyana.

Dalilin faduwar farashi

Alhaji Abdullahi Usman, Shugaban Kamfanin kayayyakin abinci na Mumin Foods Ltd, wanda a cewarsa ya fi shekara 30 yana kasuwancin riɗi, ya bayyana cewa faɗuwar farashin na da nasaba da yadda buƙatar amfanin gonar da ake nomawa a Nijeriya ta ragu matuƙa a kasuwannin duniya.

Ya ce, sai sai abin takaici, tun bayan da buƙatar kayayyakin ta ƙaru, ’yan kasuwa da dama sun riƙa fito da kuɗaɗe suna sayen kayan, ciki har da kayan abinci.

Ɗan kasuwan ya bayyana cewa saukar farashin ya ƙara nuna yadda ƙasashe suka dage wajen noma abin da za su ci, shi ya sa kasuwannin Nijeriya suka cika suka batse da kayayyaki, wanda hakan ya sa ala tilas farashinsu ya faɗi.

Ya ce “Mutane sun fito da mazajen kuɗaɗe wajen sayewa tare da ɓoye kayayyakin, duk da wasu ’yan ƙasashen waje na hankoron sayen amfanin gonar da ake nomawa a Nijeriya musamman kasancewar sun yi amanna da cewa na asali ne ba wanda aka gurɓata da sinadarai wajen noma su ba.

“Da farko dai alƙaluma sun nuna komai na tafiya yadda ake buƙata, sai mutane suka ci gaba da ƙaruwa. Sai dai abin takaici, sai buƙatar wadɗannan kayan daga kasashen ta ragu sosai, wanda hakan ne ya tilasta faɗuwar farashin kayayyakin amfanin gonar,” in ji shi.

Bayanai sun nuna cewa kilo ɗaya na riɗi wanda a bara aka sayar da shi N2,300, a yanzu ana sayar da shi N1,600. Sai kuma kilo ɗaya na zoɓo wanda shi kuma a bara yake 2,300, a bana ya dawo naira1,500. Wasu majiyoyi a harkar hada-hadar amfanin gona sun ce ana hasashen akwai yiwuwar farashin ya ci gaba da faɗuwa yayin da kasashen waje ke ci gaba da rage yawan bukatar kayan na Najeriya.

Haka kuma an yi amannar cewa faɗuwar farashin kayan abincin zai kawo sauƙi ga iyalan da ke rayuwar hannu-baka-hannu-ƙwarya na ɗan wani lokaci, ba lallai ta ci gaba da zama a haka ba. Bugu da kari, mutanen da ke sayar da wadannan kayayyakin ba su cika yin asara ba kasancewar suna da inda za su ajiye su har zuwa lokacin da farashin zai musu inda suke so.

Masana tattalin arzikin amfanin gona kuma na hasashen cewa dawowar Indiya fitar da kayan da take nomawa zuwa ƙasashen ketare, zai sa yawan buƙatar kayayyakin ta ragu a duniya, wanda hakan zai iya sawa farashin ya daɗa sauka, na daya daga cikin dalilan da suka jawo karyewar farashin a Najeriya a ’yan watannin nan.

Alhaji Abdullahi Usman, shugaban Mumin Food Limited, ya ce ƙarancin masu sayan kayan masarufin Nijeriya a cinikayyar ƙasa da ƙasa na da alaƙa da faɗuwar kayan masarufi a cikin ƙasa Nijeriya.

Ya ƙara da bayanin cewa, “Abin takaici, yadda buƙatun ’yan Nijeriya suke ƙaruwa na sayen kayan masarufi, wasu daga cikin ’yan kasuwa sun saye kayan masarufin da kayan gonar, ƙara da cigaban da aka samu kwanan nan wanda ya ba wa ’yan ƙasashe dama su inganta amfanin gonarsu kuma su rage shigowa da kayan ƙetare, ya sa farashin wasu kayan masarufi ya sauka.

“Mutane da dama suna ajiye kayan masarufi musamman a lokacin da wasu ƙasashe suka nuna suna buƙatar wani nau’i na kayan masarufi daga Nijeriya, saboda kayan masarufin Nijeriya ba su da sinadaran zamani. Amma cikin babu zato sai buƙatun waɗannan ƙasashe suka yi ƙasa wanda hakan ke da alaƙa da saukar farashin kayan masarufin.

“Bugu da ƙari, faɗuwar farashin yana kawo rangwamen wucin gadi ga masu sayen ɗai-ɗai wanda suke a gida. Amma masu ta’ammali da kayan masarufi abin ba ya shafar su, saboda suna da hanyar ajiye kayan har zuwa wani lokacin da ya yi musu,” kamar yadda ɗan kasuwan ya bayyana.

Masana noma da tattalin arziki sun tabbatar da rahoton cewa ƙasar Indiya ta dawo fitar da kayan masarufi zuwa ƙasashen ketare, a maimakon sayowa daga can, wanda hakan ke nuni da cewar za a iya samun faɗuwar farashinsu a ƙasashen da suke sayar wa da Indiya kaya.

Daga wani masanin tattalin arziki daga Kwalejin Ilimi na Sa’adatu Rimi da ke Kano, Mallam Hassan Ali, “Darajar naira da kuma dalar Amurka na taka rawar gani wajen sauƙaƙa wa al’amuran shigo da kaya.

“Haka kuma, Babban Bankin ƙasa (CBN) ya ce hadahadar canjin naira zuwa dalar Amurka yana yawo tsakanin N1,478 da kuma N1,551 daga watan 1 na Janairu, 2025 har zuwa yanzu.”

Ya bayyana cewa, “Wannan na nuni da faɗuwar sama da kaso 8% daga N1,688 da yake a ƙididdigar wasu watanni na shekarar 2024. Haka zalika, yanayin lokaci kusan shi ne ƙashin bayan hawa da faɗuwar farashi a kasuwar kayan masarufi, saboda lokacin shuka da girbi yana shafar yanayin hadahadar kayan abincin da kuma farashinsu. Kusan akwai hasashen cewa makonni bayan girbe amfanin gona (lokacin kaka) farashin kayan abinci da sauran kayan gona yana faɗuwa ƙasa saboda yawan saya da kuma fitar da su da manoma ke yawan yi a wannan lokacin.”

A Jihar Kano an samu rohoton cewa ana samun sauye-sauyen tashin farashin kayayyakin masarufi da dama, musamman canjin yanayi da ake samu da kuma yadda ake samar da kayayyakin da suka shafi amfanin gonar.

Wani manomin riɗi daga Jihar Jigawa, Alhaji Sagir Bello Black, ya sanar cewa a lokutan girbi farashin kayayyaki yana raguwa sakamakon yawan wadatar kayayyakin masarufi a kasuwa, sannan kuma yakan tashi a lokacin rani saboda ƙarancin kayayyakin.

Ya ƙara da cewa, gazawar samar da isashen kayayyakin da ’yan kasuwa ke buƙata irin na baya saboda rashin ruwan sama ko yawan ruwan sama, da tashe-tashen hankula da rashin tsaro, na haifar da hauhawar farashin kayayyakin amfanin gona.

Alhaji Aminu Gumel, wani ɗan kasuwar riɗi wanda a cewarsa ya shafe sama da shekara 30 yana kasuwancin riɗi, ya bayyana cewa ya sayi kayayyaki na miliyoyin nairori don fitarwa, amma abokan kasuwancinsa na ƙasashen waje ba su biya ba tukuna, saɓanin yadda al’amura suka kasance a shekarun baya.

Alkasim Idris Ajingi, manomin citta, ya ƙara da cewa, “A shekarar 2023 Nijeriya ta fuskanci ƙarancin noman citta sakamakon cutar ƙwari da ta lalata kusan kashi 70% na amfanin gona.”

Ya ƙara da cewa, “Wannan annoba ta kawo raguwar wadata da samuwar kayayyakin wanda ya kawo hauhawar farashin citta da ninki shida na tsawon shekaru daga N50,000 zuwa N300,000 a kowane buhu.

Ya ƙara da cewa, “Lokacin da manoma ke fuskantar matsalolin noma a wannan lokacin kuma kayayyaki ke raguwa shi ya sa farashin kaya dole ne ya tashi.”

Kayayyakin Nijeriya sun samu karɓuwa a duniya

Kayan masarufin Nijeriya sun samu karɓuwa a kididdigar kasuwar duniya. misali, likafar kasuwar kasuwar waken suya a ƙasar ta ci gaba, saboda hana shigowa da shi a 2023/2024. Bincike ya nuna yadda matakin ya taka rawar gani wajen ƙaruwar bukatar ’yan Nijeriya a kan waken suya.

Rahoto ya bayyana cewa waken suyar da ake fitarwa daga Nijeriya ya yi tashin gwauron zabo da sama da 1000%. Haka ne ya sa farashin yake ƙaruwa a cikin gida da kasuwannin ƙasa da ƙasa ya ƙaru daga USD 10.8 million a 2022, zuwa USD 201million a 2023, da farashin cikin gida wanda ya ƙaru da sama da 1 million a kowane awo.

Bugu da ƙari, bincike ya tabbatar da cewa kilo ɗin waken suya an sayar da shi akan N1,300 a shekarar da ta wuce, kuma ana sayar da shi a kan N7,500 a yanzu.

Mista Chucks Idowu, wani attajiri da ke kasuwancin waken suya ma ƙasa da ƙasa, ya ce ƙasashen da suke buƙatar waken suyar daga Nijeriya su ma suna noma tasu, shi ya sa buƙatarta a kasuwar duniyar yake raguwa.

Ya ƙara bayyana cewa, “ƙarin farashin waken suyar, a shekarar da ta gabata ya sa mutane da dama suka saya suka ajiye, kuma yanzu farashin ya faɗi, dole suka fito da shi don sayarwa a halin da kasuwa take a yanzu ko ba don komai ba, za su so su ci abinci.”

 

Daga Ibrahim Musa Giginyu, Anas Abbas da Anwar Usman Hassan, Kano