Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), ta bayyana cewa hauhawar farashi a Najeriya ya sauka zuwa kashi 22.22 a watan Yuni 2025, daga 22.97 da aka samu a watan Mayu.
Wannan shi ne karo na uku a jere da hauhawar farashi ke sauka, duk da cewa ragin ba shi da yawa ba, wato kashi 0.76 ne kacal.
Sai dai hukumar ta ce matsakaicin farashi, ya ƙaru zuwa 123.4 a watan Yuni, daga 121.4 da aka samu a watan Mayu.
Idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, hauhawar farashi a watan Yunin 2025, ya ragu da kashi 11.97, idan kuwa aka kwatanta da 34.19 wanda aka samu a watan Yunin 2024.
Amma idan aka duba watanni biyu a jere na baya, hauhawar farashi ya ƙaru da kashi 1.68 a watan Yuni, daga kashi 1.53 da aka samu a Mayun 2025.
Wannan ya nuna cewa farashin kaya ya tashi a watan da ya gabata.
A ɓangaren abinci kuwa, hauhawar farashi ya kai kashi 21.97 a Yunin 2025, inda aka samu ragi idan aka kwatanta da 40.87 a Yunin 2024.
A lissafin wata-wata kuwa, farashin abinci ya ƙaru da kashi 3.25 a watan Yuni, idan aka kwatanta da kashi 2.19 da aka samu a watan Mayu.
Wannan ƙarin farashi ya faru ne saboda tashi farashin kayan abinci kamar su wake, attaruhu, rogo, naman dabbobi, tumatir, garin ayaba da barkono.
Matsakaicin hauhawar farashin kayan abinci ya kai kashi 28.28, wanda ya ragu da kashi 7.06 idan aka kwatanta da kashi 35.35 a shekarar da ta gabata.