✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hauhawar Farashi ya ƙaru a watan Maris — NBS

NBS ta ce an samu ƙarin kashi 1.05 daga kashi 23.18 cikin ɗari da aka samu a watan Fabrairu.

Hukumar Ƙididdiga ta Nijeriya NBS ta ce hauhawar farashi ya ƙaru a ƙasar zuwa kashi 24.23 cikin 100 a watan Maris.

Alƙaluman da hukumar ta fitar sun nuna an samu ƙarin kashi 1.05 daga kashi 23.18 cikin ɗari da aka samu a watan Fabrairu.

Wannan ne karon farko da aka samu ƙarin hauhawar farashin tun bayan da hukumar ta NBS ta soma fitar da rahoton bisa sabon ma’unin tattara alƙaluma da ta fara amfani da shi a farkon shekarar nan.

Sai dai bayan soma amfanin da sabon tsarin fitar da ƙididdigar a watan jiya, NBS ta ce da wuya a iya gane haƙiƙanin raguwa ko hauhawa a yanzu.

A wani jawabi da ya yi manema labarai tun a watan da ya gabata, shugaban hukumar, Prince Adeyemi Adeniran, ya bayyana cewa sun sauya tsarin ne saboda “daidaita shi da irin na sauran ƙasashen duniya.”

Ya ce karo na ƙarshe da Nijeriya ta sauya tsarin ƙididdigar shi ne a shekarar 2009, inda ake ƙididdige farashin kayan da aka fi amfani da su a wannan tsakanin.

Hakan na nufin yanzu za a riƙa kwatanta farashin kayayyakin da aka ƙididdige daga shekarar 2024, maimakon 2009 da aka riƙa amfani da ita a baya.

A sabbin alƙaluman da NBS ta fitar, ta alaƙanta hauhawar farashin da tashin kayayyaki irinsu citta, garin rogo, shinkafa, zuma, dankali, barkono da sauransu.

“Bugu da ƙari, alƙaluman saurin hauhawaar farashin ya kai 3.90% a watan Maris na 2025 idan aka kwatanta da na Fabrairu, wanda yake 2.04%” a cewar rahoton.

Ta ƙara da cewa, bisa lissafin shekara-shekara, hauhawar kayan abinci kuma ta kai kashi 21.79 a watan Maris ɗin na 2025 idan aka kwatanta da Maris na 2024.

Ta ce abubuwan da suka fi jawo hauhawar farashin sun haɗa da abinci da kuma lemukan sha na kwalaba (kashi 9.28 cikin 100), da kuɗaɗen hayar gida da na wuraren sayar da abinci (kashi 2.99 cikin 100), da kuɗin sufuri ((kashi 2.47 cikin 100).

Sauran su ne kuɗin ruwa, wuta, iskar gas da sauran makamashi, ilimi, sai kuma harkokin lafiya.

Aminiya ta ruwaito cewa, Hukumar NBS ta ce alƙaluman hauhawar farashi sun koma kashi 24.48 daga 34.8 cikin 100 a watan Janairun da ya gabata.