✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama ɗan Najeriya yana taimaka wa Rasha a yaƙinta da Ukraine

Mutumin ya shafe shekaru huɗu yana zaune a ƙasar Rasha kafin a kama shi akan laifin da ke da nasaba da miyagun ƙwayoyi.

Sojojin Ukraine sun kama wani ɗan Nijeriya da ke taimaka wa Rasha a yaƙin da suke gwabzawa sama da shekaru biyu biyo bayan mamayar ƙasarsu.

Wani bangaren sojin da ke ƙunshe da mayaƙan Rasha da ke goyon bayan Ukraine a wannan yakin, wanda ake kira ‘Freedom Of Russia Legion ne ya kama Kehinde Oluwagbemileke mai shekaru 29 a yankin Zaporizhzhia bayan shafe watanni biyar yana yaƙi a cikin mayaƙan Rasha.

Oluwagbemileke ya shafe shekaru huɗu yana zaune a ƙasar Rasha kafin a kama shi akan laifin da ke da nasaba da miyagun ƙwayoyi.

An ruwaito cewa matashin ya amince ya shiga wannnan yaƙi ne domin a rage masa yawan shekarun da zai shafe a gidan yari sakamakon laifin da aka kama shi da shi.

Gbemileke yana daga cikin dubban sojojin haya daga ƙasashe masu tasowa da ke taimaka wa Rasha a yaƙinta da Ukraine.