✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ruwa da iska sun kashe mutum 5, sun raba sama da 5,000 da muhallansu a Yobe

Ruwan sama kamar da bakin kwarya hade da iska sun yi ajalin mutum biyar sannan wasu 92 suka samu munanan raunuka a kananan hukumomi bakwai…

Ruwan sama kamar da bakin kwarya hade da iska sun yi ajalin mutum biyar sannan wasu 92 suka samu munanan raunuka a kananan hukumomi bakwai na jihar Yobe.

Shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar (SEMA) Dr Goje ne ya tabbatar da hakan a ranar Laraba a Damaturu.

Ya ce iftila’in ya shafi al’ummomi 48 ne a fadin kananan hukumomin da lamarin ya faru.

Dr Goje yan kuma ce bala’in ya shafi gidaje 1,264, tare da raba mutum 5,022 da muhallansu.

Shugaban ya kuma ce hukumarsa tare da hadin gwiwar kungiyar bayar da tallafi ta kasa da kasa ACF tare da tallafi daga ofishin kula da harkokin wajen Jamus (GFFO), sun raba kayan agajin ceton rai ga magidanta 566 a kananan hukumomin Fika da Potiskum da lamarin ya shafa.

Kazalika, kididdigar haɗin gwiwa ta hukumar ta SEMA da ACF suka fitar ta ba da fifiko ga iyalan da wadanda wannan iftila’i ya fi shafa kai tsaye musamman waɗanda suka rasa gidajensu, da kayan masarufi, ko damar samun wani taimakon na tsafta.

Mohammed Liman Kingimi, na kungiyar ACF, ya tabbatar da kudurin kungiyar na kara ba da taimako bisa ga yadda bukatun hakan suka taso.

Ya ce kungiyar na kuma shirye-shiryen kaddamar da tallafin abinci ga magidanta 566 don rage musu radadi.

Dokta Goje ya buqaci wadanda suka ci gajiyar tallafin da su yi amfani da shi yadda ya kamata sannan ya jaddada kudirin gwamnatin jihar na kare al’umma masu rauni ta hanyar xaukar matakan gaggawa.

Ya kuma jaddada qudirin hukumar cewa kullum a shirye take wajen gudanar da ayyukanta kamar yadda ya dace.