Rundunar ‘Yan Sandan jihar Bauchi ta ce ta kama wata budurwa ‘yar shekara 19 mai suna Esther Gambo bisa zargin sace yara da yin garkuwa da su sannan ta kashe su.
Rundunar ta ce wadannan kananan yara biyu mata ne ‘yan shekara bakwai, lamarin da ya jawo tarzoma da kona coci.
Kakakin Rundunar, CSP Mohammed Ahmed Wakil ya shaida wa manema labarai haka a Bauchi ranar Alhamis.
Wakil Ya bayyana cewa an samu rahoton faruwar lamarin ne a ranar 22 ga watan Yulin 2025, da misalin karfe 3:00 na rana.
Ya ce, “Wata matashiya mai shekara 19 mai suna Esther Gambo daga ƙauyen Lemoro da ke karamar hukumar Toro a jihar Bauchi ta yaudari wasu yara mata biyu ‘yan shekara bakwai, Khadija Sama’ila da A’isha Dahiru daga ƙauyen Unguwan Sarkin Yaki. Daga bisani Bayan ta shiga dasu daji sai ta sa adda ta kashesu a wat gonar masara.
“Da samun wannan labarin sai ’yan sanda tare da ’yan banga suka bazama neman matar a cikin dajin, kuma sun yi nasarar ƙwato gawarwakin yaran matan da suka rasu, sun kama Esther Gambo, tare da kuɓutar da wata jaririyar da aka yi garkuwa da su,” in ji Wakil.
Kakakin ’Yan Sandan, ya kuma ce binciken farko ya nuna cewa wacce ake zargin Esther Gambo ta lallaɓa ‘yan matan ne da nufin samun sabuwar haihuwa mace da za ta kai wa wata mata mai suna Nafisa Dahiru.
Bayan da ta samu jaririyar, sai Esther ta kai ‘yan matan biyu data sato zuwa gonar masara da ke kusa, inda ta kashe su da adda kafin ta gudu daga wurin.
Wakil ya ce, “Bayan faruwar wannan lamari, tashin hankalin jama’a ya ɓarke, galibi tsakanin matasan Musulmin yankin, wanda ya haifar da mummunar zanga-zanga, ciki har da ƙona coci-coci, da yunƙurin ƙona ofishin ‘yan sanda da ke Garin Tulu.
“Sai da aka tura ƙarin jami’an tsaro daga rundunar ‘yan sandan yankin Toro da kuma sassan da ke maƙwabtaka da su domin dawo da zaman lafiya, inda suka yi nasarar daƙile tarzomar. A sakamakon wannan tashin hankalin, an kama mutum 16 da ake zargi da hannu a cikin lamarin.
“Wadanda ake zargin da aka kama su ne Abbas Abdullahi mai shekaru 20, Mubarak Auwal mai shekaru 19, Abdullahi Muhammad DA Ake kira P.A), mai shekaru 19, Dauda Abdullahi mai shekaru 19, Abubakar Sama’ila, mai shekaru 18, Ibrahim, Auwal mai shekaru 18, Abdulmutallib mai shekaru 18 Abdulrahman Ibrahim, mai shekaru 17.
“Sauran wadanda ake tuhuma sun hada da Abdulwahid Sulaiman, mai shekaru 17, Salihu Shuaibu, mai shekaru 20 , Sirajo Halliru, mai shekaru 24, Musayib Abdullahi, mai shekaru 21 , Ibrahim Abubakar , 19 , Esther Idi, 19, Gambo Yakubu, Mai Shekaru 20 da Idi Bitrus, Mai Shekaru 50,” in ji Kakakin.
Wakil ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, CP Sani-Omolori Aliyu, ya jaddada muhimmancin kiyaye doka da kuma tabbatar da zaman lafiya a jihar Bauchi.
Ya nuna damuwarsa kan ayyukan baya-bayan nan da ke kawo cikas ga bin ƙa’idojin shari’a tare da yin kira ga al’umma da su guji daukar doka a hannunsu.
Ya kuma tabbatar wa da jama’a cewa ana gudanar da cikakken bincike tare da kiran da kowa ya kwantar da hankalinsa domin an shawo kan lamarin yadda ya kamata.