Ɗaruruwan ɗalibai ne suka suka tsallake rijiya da baya a lokacin da ajujuwan da suke rubuta jarabawar kammala sakandare (SSCE) suka rufta a ranar Laraba.
Lamarin ya faru ne a makarantar sakandiren gwamnati da ke Namne a Ƙaramar hukumar Gassol a Jihar Taraba.
- Ko kwabo ban ciyo bashi ba tun da na zama Gwamnan Kaduna – Uba Sani
- Ambaliyar ruwa ta kashe sama da mutum 50 a Neja
Ajujuwan sun rufta musu a lokacin da aka yi ruwan sama kamar da baƙin ƙwarya da iska.
Ɗaliban da masu kula da jarrabawar sun maƙale a cikin ajujuwan da suka rufta na tsawon sa’o’i kafin wasu mazauna garin su kuɓutar da su.
Wani mazaunin garin Alhaji DanAzumi Lauris ya shaida wa Daily Trust cewa, ajujuwan sun ruguje karo na biyu da ɗalibai, lokacin da rukunin farko ya gama jarabawa ya bar harabar makarantar.
Ya ce, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 6 na yammacin Laraba.
DanAzumi, ya bayyana cewa, an kai ɗalibai da malaman da suka jikkata zuwa cibiyar kiwon lafiya a matakin farko da ke kusa da makarantar inda yanzu haka suke samun kulawa.
Ya ce, baya ga makarantar, guguwar ta lalata gidaje da dama a cikin unguwar .
DanAzumi ya bayyana cewa, an kai ɗaliban da Malamai da kuma masu yi wa ƙasa hidima da suka jikkata zuwa cibiyar kiwon lafiya a matakin farko da ke kusa daga makarantar inda yanzu haka suke samun kulawa.
Ya ce baya ga makarantar da guguwar ta lalata gidaje da dama a garin.