Gwamnatin Yobe ta bayyana shirinta na mayar da tubabbun mayaƙan Boko Haram cikin al’ummarsu da aka yi wa shirin kawar da tsattsauran ra’ayi, gyara da sake haɗewa da iyalansu ƙarƙashin rundunar Operation Safe Corridor (OPSC).
Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ne ya bayyana haka a ranar Alhamis a Damaturu lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar rundunar OPSC ƙarƙashin jagorancin babban hafsan tsaron Nijeriya Janar Christopher Musa.
- Hisbah ta warware rigingimu 565 da lalata katan 51 na barasa a Yobe
- Trust Radio 92.7FM za ta fara shirye-shiryen gwaji
Gwamna Buni, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Alhaji Idi Gubana ya bayyana ziyarar a matsayin wata dama ta tuntuɓar juna da haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da gwamnatin jihar.
Ya koka da yadda rikicin da aka kwashe sama da shekaru 15 ana yi ya laƙume rayukan dubban mutane a Yobe, da lalata dukiyoyin jama’a da na masu zaman kansu tare da raba magidanta da dama da garuruwansu na asali.
Gwamnan ya ce gwamnatin jihar ta gane cewa, ba dukkan ’yan ƙungiyar ta’addancin ne ke shiga cikin kisan kai ba, yana mai cewa tsarin kishin ƙasa ya ba da damar ceto da kuma mayar da waɗanda suka nuna nadama ya zuwa ga al’ummominsu.
“Mun yi imanin cewa, an tura wasu mutane shiga cikin ’yan ta’adda ta hanyar ƙarfi ko koyarwar aƙida.”
“Tare da ci gaba da ƙoƙarinsu, za su iya tuba, gyarawa da komawa rayuwa ta yau da kullun a matsayin ‘yan ƙasa da ke da ‘yanci.” In ji Buni.
Gwamnan ya ce tubabbun ‘yan Boko Haram 390 da suka haɗa da ‘yan asalin Jihar Yobe 54 ne za su kammala karatu tsakanin ranakun 14 zuwa 19 ga Afrilu.
Ya ce, jihar ta samar da wasu tsare-tsare ta hanyar ma’aikatar Jinƙai da kula da bala’o’i domin tabbatar da sake dawo da su cikin al’umma yadda ya kamata.