Hukumar Hisbah ta Jihar Yobe ta ce, ta warware rigingimu 565 a cikin watanni 12 da suka gabata a jihar.
Wannan hukuma dai gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ne ya kafa ta a watan Maris, 2024 a wani ɓangare na ƙoƙarin magance munanan ɗabi’u a jihar.
Shugaban Hukumar ta Hisbah, Dakta Yahuza Hamza Abubakar, ya ce matsalolin da aka warware sun haɗa da batutuwan da suka shafi: Harkar iyali da kasuwanci da gado da kuma basussuka.
Sauran matsalolin da hukumar ta Hisbah ke warwarewa sun haɗa da: Matsalolin da haddasa rikicin manoma da makiyaya da kuma rashin biyan kuɗin haya.
A cewarsa, an warware akasarin shari’ar ta hanyar sulhu da fahimtar juna.
Dokta Hamza ya ce, jami’an hukumar sun kuma ƙwace kwalayen barasa guda 56 da kuma 18 na sinadaran fosters na methylene chloride chemical (Madarar Sukurdai) a faɗin jihar.
Ya ce, addinin Musulunci da dokar da ta kafa hukumar a shekarar 2024 ta haramta sayar da barasa da sauran kayan maye a jihar.