✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cikin makonni kaɗan Obasanjo ya murƙushe Boko Haram — Atiku

Atiku ya ce shugabannin yanzu sun gaza ɗaukar matakan da suka dace wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro.

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya ce tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo ne ya murƙushe ƙungiyar Boko Haram lokacin da ta fara bayyana a shekarar 2002.

Atiku, wanda ya yi mataimakin shugaban ƙasa daga 1999 zuwa 2007, ya bayyana hakan ne a wata ganawa da masu ruwa da tsaki daga Jihar Kogi a birnin Abuja.

Ya bayyana cewa lokacin da Boko Haram ta fara tayar da hankali a Jihar Yobe, Obasanjo ya kira shi domin neman shawararsa.

Atiku, ya bayar da shawarar a kira shugabannin tsaro a ba su wa’adin daƙile lamarin, ko su sauka daga muƙamansu.

Obasanjo ya amince, ya kira su, ya ba su umarnin ɗaukar matakin gaggawa.

Atiku, ya ce cikin makonni kaɗan, dakarun tsaro suka murƙushe ƙungiyar Boko Haram a Yobe, kuma ba ta sake bayyana ba har sai da suka bar mulki.

Atiku, ya soki shugabannin da suka biyo bayan gwamnatinsu, inda ya bayyana cewa sun gaza ɗaukar matakin da ya dace kan matsalar tsaro.

“Babu ƙwarin gwiwar siyasa daga shugabanni,” in ji shi.

“Mutane na mutuwa, amma shugabanni ba su damu ba. Wannan babbar gazawa ce a hakar shugabanci.”