✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum ɗaya ya rasu a rikicin manoma da makiyaya a Yobe

Tuni rundunar 'yan sandan jihar ta gayyaci shugabannin ɓangarorin domin tattaunawa kan rikicin.

Wani rikici da ya ɓarke tsakanin manoma da makiyaya a ƙauyen Chikuriwa da ke Ƙaramar Hukumar Nangere a Jihar Yobe, ya yi sanadin mutuwar mutum ɗaya tare da jikkata wasu.

Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya faru ne da yammacin ranar Litinin, 13 ga watan Mayu, 2025 bayan da wani makiyayi ya shigar da shanunsa cikin gonar wani manomi, abin da ya tayar da rikici.

A lokacin da rigimar ta ɓarke, an harbi wani manomi mai suna Babayo Maina Osi da kibiya a goshinsa, wanda hakan ya jikkata shi.

Wata majiya daga ƙauyen ta ce rikicin ya ƙazanta sosai har ya rikiɗe zuwa faɗa tsakanin manoma da makiyaya.

A lokacin wannan faɗa ne aka harbi wani mutum mai suna Usman Mohammed, mai shekara 35 da kibiya, wanda daga bisani ya rasu a Babban Asibitin Nangere.

Jami’an tsaro sun isa wajen domin daƙile rikicin da kuma hana ya ƙara rincaɓewa.

Rahoton ya bayyana cewa an ƙwato shanu biyu, awaki 29 da raguna daga hannun manoman da ake zargi sun ƙwace daga hannun makiyaya.

A yanzu haka, an gayyaci shugabannin ɓangarorin biyu domin tattaunawa da kuma tabbatar da cewa irin wannan rikici bai sake faruwa ba a nan gaba.

Duk ƙoƙarin da wakilin Aminiya ya yi don jin ta bakin kakakin ‘yan sandan jihar, DSP Dungus Abdulkareem, ya ci tura, domin bai daga wayarsa ba.