✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu wanda zai manta da gudunmawar da Wike ya ba ni — Fubara

Gwamnan ya ce magoya bayansa sun rungumi sulhu su zauna lafiya da kowa.

Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya ce zai iya yin komai muddin hakan zai kawo zaman lafiya da ci gaba a jiharsa.

Fubara, ya faɗi haka ne a garin Fatakwal a ranar Asabar, yayin da yake magana da magoya bayansa.

Ya tabbatar musu cewa ya sasanta da Tsohon Gwamnan jihar, wanda a yanzu Ministan Abuja ne, Nyesom Wike.

Ya ce ya san wasu daga cikin magoya bayansa ba za su ji daɗin sasancin da aka yi ba, amma ya roƙe su da su yi haƙuri.

Ya ce: “Wani lokaci sai an ɗauki matakai masu wahala domin a samu gyara.”

Ya ƙara da cewa: “Kowa ya san mun yi iya ƙoƙarinmu. Amma yanzu abin da muke buƙata shi ne zaman lafiya.”

Fubara ya ce ba wanda zai iya musanta irin taimakon da Wike ya masa.

“E, mun samu saɓani a wasu abubuwa, amma ba za a iya cewa Wike bai taka rawar gani ba.

“Duk wanda ke sona da gaskiya, ya daina magana, lokaci ne na zaman lafiya.”