✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Yobe ta sayo hatsi don tunkarar kakar bana

Wannan shiri ya ƙara jaddada ƙudirin gwamnatin Jihar Yobe na inganta samar da abinci da kuma baiwa manoma damar bunƙasa harkokin su na noma da…

Gwamnatin Jihar Yobe ƙarƙashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni  ta sayo ton 2,000 na hatsi iri-iri domin ƙarfafa samar da abinci da kuma tabbatar da shirin tunkarar kakar bana a matsayin gudun ko ta kwana.

A cikin wata sanarwa da Yusuf Ali, mai bada shawara ta musamman kan harkokin dabarun sadarwa na zamani (SSA) ga gwamna Buni ya ce,  Kwamishinan ma’aikatar noma da albarkatun ƙasa, Ali Mustapha Goniri, ya kai ziyarar duba irin hatsin a shagunan bunƙasa noma na jiha  da ke kan titin Gujba da ke Damaturu.

Da yake zantawa da manema labarai a yayin ziyarar, Ali Mustapha ya bayyana kyakkyawan fata game da shirin, inda ya jaddada cewa za a raba hatsin ga jama’ar Yobe a cikin gaggawa ko kuma lokacin bazara domin rage matsalar ƙarancin abinci.

Baya ga hatsin, Kwamishinan ya bayyana cewa gwamnati ta sayo nau’o’in sinadarai iri-iri domin tallafa wa manoman rani da kayan lambu.

Ya kuma bayyana shirin raba irin rogo ga manoma a fadin jihar, da nufin farfaɗo da noman na rogo lura da amfanin da ake yi da ita ta fuskoki iri-iri na abinci har ma da sarrafa ta da ake yi ya zuwa garin fulawa don yin abubuwa da ita.

Kwamishinan ya yabawa gwamnatin Gwamna Mai Mala Buni, bisa jajircewa da goyon baya da take bayarwa wajen bunƙasa harkar noma a Jihar Yobe.

Tawagar binciken ta haɗa da babban sakataren ma’aikatar, Barista Muhammed Inuwa Gulani da daraktoci da sauran jami’an ma’aikatar.

Wannan shiri ya ƙara jaddada ƙudirin gwamnatin Jihar Yobe na inganta samar da abinci da kuma baiwa manoma damar bunƙasa harkokin su na noma da nufin samar da ishasshen abinci a faɗin jihar.