✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sallah: Mun shirya samar da tsaro a Yobe — ’Yan Sanda

Rundunar ta ce za ta saka ƙafar wando ɗaya da duk wanda zai tayar da hankali a jihar.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Yobe, ta ce ta shirya tsaf domin tabbatar da tsaro a lokacin bukukuwan Sallah da ke tafe.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Emmanuel Ado, wanda mataimakinsa DCP Saleh Sama’ila ya wakilta, ya bayyana haka ga manema labarai bayan zaman kwamitin tsaron jihar da aka gudanar a Damaturu.

Taron ya samu jagorancin sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Baba Malam Wali, a madadin Gwamna Mai Mala Buni.

A cewar CP Emmanuel, rundunar ‘yan sandan tare da sauran hukumomin tsaro sun ɗauki matakan da suka dace don kare rayuka da dukiyoyin al’umma, sai dai fatan su shi ne Allah Ya sa komai ya tafi lafiya.

Ya ƙara da cewa an tura jami’an tsaro zuwa kowane yanki na jihar tare da umarnin su saka ido sosai da kuma ɗaukar mataki cikin gaggawa idan aka ga wata barazana ga zaman lafiya.

Rundunar ta buƙaci jama’a da su yi bukukuwan Sallah cikin kwanciyar hankali ba tare da tayar da wata fitina ba.

Hakazalika, rundunar ta ce ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen hukunta duk wanda ya nemi tayar da hankali a cikin al’umma.

Taron ya samu halartar babban mai bai wa gwamna shawara kan harkokin tsaro, Birgediya Janar Dahiru Abdulsalam (mai ritaya), da sauran manyan jami’an tsaro daga hukumomi daban-daban a jihar.