✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamna Buni ya tallafawa iyalan sojojin da suka mutu 

Gwamnan ya jajanta wa sojoji da iyalan ma’aikatan da suka mutu, yana mai cewa, “Jami’an ba su mutu a banza ba, sun mutu suna ƙoƙarin…

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni a ranar Alhamis ya ziyarci sojojin Hedikwatar Task Force Brigade ta 27 Buni Gari, domin jajantawa waɗanda aka kashe kan harin da ’yan tada ƙayar baya suka kai. 

A cikin jawabinsa Gwamna Buni ya bayyana cewa, abin takaici ne ga sake ɓarkewar tashe-tashen hankula da kuma hare-haren da ake kaiwa jami’an tsaro.

Gwamnan ya jajanta wa sojoji da iyalan ma’aikatan da suka mutu, yana mai cewa, “Jami’an ba su mutu a banza ba, sun mutu suna ƙoƙarin kare ƙasarsu sosai”.

Ya bayar da tallafin Naira miliyan 2m ga kowane iyalan jaruman da suka mutu, sannan kuma Naira miliyan 1m ga jami’an da suka samu raunuka.

Buni ya ce, gwamnati za ta kuma bayar da tallafin ilimi kyauta ga yaran sojojin da suka mutu.

Hakazalika, Gwamnan ya sanar da bayar da gudunmuwar Naira miliyan 50 da za a raba wa dakarun rundunar ta 27 Brigade Buni Gari, baya ga kayan abinci, katifa, barguna da sauran kayayyaki da gwamnatin jihar ta bayar.

Ya kuma ba da tabbacin goyon bayan gwamnati da al’ummar jihar ga sojoji da sauran jami’an tsaro domin yaƙar waɗannan ’yan ta’addan yadda ya kamata tare da fatattakarsu.

Gwamna Buni ya ba da umarnin ƙarfafa tsaro a kewayen rundunar, inda ya ba da tabbacin goyon bayan gwamnati ga jami’an tsaro, “Za mu ci gaba da ƙara ƙaimi wajen inganta tsaro a kewayen.

Kwamandan rundunar Birgediya Janar Usman Ahmed, wanda ya jagoranci Gwamnan wajen duba wannan runduna, ya yabawa Gwamna Buni kan yadda ya ke nuna damuwa da kulawa ga sojojin a kowane lokaci.