Shirin Samar da Abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya (WFP) ya sanar da dakatar da bayar da tallafin abinci a ƙasashen Yammaci da Tsakiyar Afirka da ke fama da rikici.
Hakan dai na zuwa ne a sakamakon rage tallafin da Amurka ke bayarwa na kuɗi ƙarƙashin Hukumar USAID, wanda hakan ke kawo cikas ga ayyukan wannan ƙungiyar.
Duk da cewa lokaci ya bambanta daga ƙasa zuwa ƙasa, ana hasashen kayan abinci za su isa zuwa kusan watan Satumba a mafi yawan ƙasashen da abin ya shafa, wanda hakan zai bar miliyoyin mutane masu rauni cikin halin rashin tallafin gaggawa, a cewar WFP.
“Muna yin duk mai yiwuwa don fifita ayyukan da suka fi muhimmanci wajen ceton rayuka, amma ba tare da samun goyon bayan gaggawa daga abokan hulɗarmu ba, damar mu na amsa buƙatu tana raguwa kowace rana.
“Muna buƙatar ci gaba da samun kuɗaɗe don tabbatar da ci gaba da rarraba abinci da kuma kiyaye fata,” in ji Margot van der Velden, daraktar yanki a WFP a tattaunawarsa da Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press.
Ƙasashe bakwai ne abin ya shafa a wannan yanki, inda dakatar da ayyuka ya riga ya fara a Mauritaniya, Mali, da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, inda ake hasashen kayan abinci za su isa na ‘yan makonni kaɗan kawai.
Alƙaluman sun nuna cewa rabon tallafi ya ragu sosai a sansanonin ‘yan gudun hijira na Nijeriya da ke Kamaru, a cewar WFP.
A cewar bayanan WFP da AP ta gani, ana hasashen lamarin zai yi tasiri kan miliyoyin mutane kai tsaye, ciki har da yara 300,000 a Nijeriya da ke cikin hatsarin shiga halin “matsanancin ƙarancin abinci mai gina jiki, wanda zai iya ƙara haɗarin mutuwa.”
WFP ta ce tana buƙatar dala miliyan 494 domin samar da abinci a rubu’i na biyu na shekarar 2025, amma kuɗaɗen sun ƙare gaba ɗaya, wanda hakan ya tilasta ta fifita rukunin mutane masu rauni.
A Arewa da Tsakiyar Mali, za ta fifita ‘yan gudun hijira da aka kwashe kwanan nan da kuma yara ‘yan ƙasa da shekaru biyar.