✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsadar rayuwa ta sa ’yan Nijeriya na siyan abincin da ya lalace

Dubban mutane na rububin siyan kayan abincin da lokacin amfaninsu ya ƙare, kamar abincin yara da madarar jarirai zuwa abincin gwangwani da lemukan kwalba da…

Tsadar rayuwa ta sa ’yan Nijeriya amfani da kayayyakin da wa’adin amfani da su ya ƙare, lamarin da ya jefa mutane da dama cikin hatsari.

Wani da ya samu kansa a cikin irin wannan hali shi ne Bitrus da ke Maidugurin Jihar Barno, wanda bayan kammala aikinsa na yau da kullum gab da almuru, ya koma gida a gajiye, ga kuma yunwa, inda ya ji cikinsa ya fara ƙugi.

Kawai sai ya garzaya wani ɗan shago a bakin hanya ya sayo ƙaramar robar madarar yogot da kuma biskit domin rage yunwar da ta taso, kafin ya ci abincin dare. Sayen su ke da wuya, ya buɗe robar ya fara kwankwaɗar madarar, yana haɗawa da biskit ɗin a hanya, kafin ma ya koma gida.

Ba a yi awa guda da hakan ba sai Bitrus ya fara jin cikinsa ya murɗa, alamar akwai matsala. Da raɗaɗin ya ƙara tsanani sai ya ji zufa na keto masa, ya rasa inda zai sa kansa.

Ana cikin haka sai ya dubi jikin robar, sai ya ga ashe wa’adin amfanin madarar ya jima da ƙarewa. Ga shi ya riga ya gama da biskit ɗin har ya jefar da ledar, don haka bai san ko shi ma ya lalace ba.

Ana cikin haka sai cikinsa ya tsure ya fara gudawa, kuzarin jikinsa ya ragu matuƙa, alamar ruwan jikinsa ya yi ƙasa. A sakamakon haka sai da aka kwantar da shi a asibiti mafi kusa a unguwar, inda likitoci suka tabbatar cewa gubar abinci ce ta haddasa masa matsanancin ciwon ciki.

Bitrus ɗaya ne daga cikin mutanen da suka tsallake rijiya da baya, bayan cin abinci ko kayan da suka lalace, da ake sayarwa wasu shaguna a ƙasar nan. Yana kuma cikin ’yan Nijeriya da suka amsa kiran da wannan jarida ta wallafa a shafinta na sada zumunta na WeekendTrust a ranar 12 ga Maris, 2025, inda aka buƙaci mutane su bayar da labaransu kan saye ko kuma amfani da kayan abinci da wa’adinsu ya ƙare.

Kasuwar Bonanza: Cibiyar kayan da suka lalace

A kan haka ne wakilinmu ya yi binciken ƙwaƙwaf a wata kasuwa a ɗaya daga cikin manyan unguwanni a Yankin Birnin Tarayya, inda dubban mutane ke rububin sayen kayan da lokacin amfaninsu ya ƙare, kamar abincin yara da madarar jarirai zuwa abincin gwangwani da lemukan kwalba da sauran kayan amfanin gida.

Kasuwar Bonanza da ke Mararaba a Jihar Nasarawa, wadda wata katafariyar kasuwa ce ga masu ƙaramin ƙarfi, kuma ta samo sunanta ne daga yadda kayan da ake sayarwa ke da tsananin araha.

Wannan kasuwa tana maƙwabtaka da dubban ma’aikata a Abuja da ke sauka a Nyanya, Mararaba, Masaƙa da sauran garuruwa da ke kusa da hanyar Abuja-Keffi a cikin Jihar Nasarawa, wadda ta zama matsugunin masu matsakaici da ƙaramin ƙarfi da ’yan kasuwa masu ƙananan sana’o’i da ke aiki a Abuja.

Duk da cewa kasuwar na da cunkoson jama’a, ranakun Lahadi, takan cika maƙil, saboda yawancin mazauna waɗannan unguwanni sukan yi wa Kasuwar Bonanza da ke Mararaba tsinke, saboda ita ce ranar kasuwar, inda ’yan kasuwa ke baje kolin hajojinsu — daga kayan abinci da kayan kwalliya da kayan amfanin gida a kan tebura da sauransu.

Sukan kasa kayan abinci da sauran kayan da lokacin amfaninsu ya wuce, inda suke janyo hankalin masu siyayya, waɗanda yawanci ba su lura da wa’adin amfanin da aka buga a kan kayan.

Wakilinmu ya lura cewa, yawancin kayan da aka kasa a kan teburan sun riga sun lalace, amma masu siye na ganin cewa, kayan ba su da illa duk da cewar lokacin amfani da su ya wuce.

Masu sayen abincin jarirai da ya lalace

A yayin binciken sirrin da wakilinmu ya yi a Kasuwar Bonanza, domin sanin ainihin abin da ke faruwa, ya ga wani wuri ya cika da ’yan kasuwa da ke sayar da kayayyaki iri-iri.

A nan ne ya fara lura cewa, “tsananin buƙata da matsin tattalin arziki” na daga cikin abubuwan da ke tilasta wa mata da magidanta zuwa kasuwar su sayi madarar jarirai da sauran kayan yara da suka lalace, saboda sauƙin farashin kayan fiye da yadda ake sayarwa a sauran kasuwanni.

Wata mata da wakilinmu ya gani ta riƙe robar madarar yara mai nauyin giram 25 da kuma gwangwanin madarar yara daga haihuwa zuwa wata 12, ta shaida wa abokiyar tafiyarta cewa, “Ba ni da zaɓi,” saboda ba za ta iya sabbin kayan abincin yaran ba.

A yayin da matar take wannan magana, tana kuma ƙoƙarin samun wasu ƙarin kayan abincin yara da suka wuce lokaci saboda arharsu.

Mutane na sayen madara da hatsi da kayan miya ɗan kamfani ba tare da damuwa da cewa wa’adin amfanin kayan ya shuɗe ba. Wakililmu ya ji ɗaya daga cikin wasu da suka je sayayya a kasuwar yana ce wa abokan tafiyarsa kamfanonin: “Sun dai rubuta ranar ƙarewar wa’adin aikin kayan ne, amma ko ka ci, babu abin da zai same ka,” sauran kuma suna gyaɗa kai da ke nuna amincewarsu da maganar.

Sakamakon arhar kayan da kuma rashin ƙarfin sayen waɗanda da suka cika ƙa’ida, masu sayayya suna ganin cewa kasuwar tana ba su zaɓin samun abinci da kayan masarufi masu araha da sauƙin samu.

Wani magidanci ya shaida wa wakilinmu cewa, “Abin da za mu iya saya ke nan.” Shaidar rashin damuwarsu da ƙarewar wa’adin kayan a bayane take, duba da yadda suke cika jakunkunansu da irin waɗannan kaya da suka saya, duk da illar da kayan za su iya yi ga lafiyarsu ba.

Araha ba ta ado

Wakilinmu ya sayi fakitin abincin yara mai nauyin 454g wanda ya wa’adinsa ya ƙare tun a watan Oktoba 2024 a kan N800, alhali a kasuwa yana kaiwa N9,000 zuwa N12,000. Haka kuma, ya sayi leda 10 na hatsi (25g kowanne) wanda wani sanannen kamfani ya sarrafa wanda shi kuma wa’adinsa ya ƙare a watan Agusta 2024, a kan N80 kowanne, duk da cewa N300 kowace leda take a kasuwa.

Yayin da wakilin namu yake ƙoƙarin sayen wani abincin yara masu shekaru mai nauyin 300g, ya lura da wata mace a gefe tana jiran kayan cikin damuwa, saboda da alamar ita ma tana son saya, ga shi kuma wanda ɗan jaridar ya ɗauka shi ne na ƙarshe a kan teburin.

Da ya duba sai ya gano cewa lokacin amfanin abincin ya ƙare tun a watan Agustan 2024, amma ganin cewa ƙarshenta jariri za a ba wa, idan har ya bari matar nan ta saya, haka nan ya saye kayan a kan N1,200 — inda ya samu sauƙin fiye da kashi 400 bisa 100 na ainihin farashinsa a kasuwa (N6,000 zuwa N8,000).

Cin abinci da wa’adinsa ya ƙare na iya kisa — Likita

Shugaban Sashen Abinci a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Jabi, Abuja, Dakta Ugwu Cosmos, ya gargaɗi jama’a game da cin kayan abinci da wa’adin amfaninsu ya ƙare, domin zai iya jawo manyan matsalolin lafiya har ma da cututtuka masu kisa.

Cosmos ya ce kayayyakin suna samun sauye-sauyen sinadarai masu illa kuma suna ɗauke da ƙwayoyin cuta masu haɗari irin su Shigella, E. coli, da Salmonella waɗanda kan haifar da munanan cututtuka kamar kwalara ko ma kisa.

Game da madarar jarirai, ya ce tsarin narkar da abinci da kuma garkuwan jikin jarirai na da rauni sosai, don haka sun fi saurin samun lahani, kamar gudawa da rashin gina jiki da cutar kwashiorkor da kuma gazawar koda a cikin yara.

“Iyayen suna ganin suna rage kashe kuɗi ne, amma a gaskiya suna jefa rayuwar ’ya’yansu cikin hadari,” inji shi.

Ya shawarci iyaye da su guji amfani da irin madarar, su koma amfani da abincin da ake samarwa a cikin gida, tare da neman shawarar ƙwararru kan ciyarwa.

Taƙaddamar ’yan kan kayan da suka lalace

Josephine Igah (ba sunanta na gaskiya ba), mazauniyar Mararaba ta samu saɓani da ’yar uwarta Mercy (ba sunanta na asali ba), kan yadda take yawan sayen irin waɗanan kayan abinci. Mercy na yawan sayen irin waɗannan kayan abinci a Bonanza Market saboda araharsu.

“A ganin Mercy, sayen kaya masu araha dabara ce ta ajiye kuɗi. Tana sayen madara, cornflakes, sukari, kayan ƙamshi, har ma da audugar mata da araha sosai a kasuwar,” in ta.

Josephine ta shaida wa wakilin namu cewa, ita ma ta taɓa shan lemun kwalba da Mercy ta sayo, ba ta lura ba, har sai da wani abu ya faru daga baya a watan Nuwamba 2024.

Ta ce ’yar uwarta ce ta kawo, ita kuma ba tare da ta duba wa’adin amfaninsa ba ta sha. Jim kaɗan bayan nan, ta fara jin ciwon ciki mai tsanani sannan gudawa ta biyo baya.

Josephine ta ce, ba ta yi zaton wa’adin amfanin lemun ya ƙare ba; ta yi tunanin tsamin lemun ne ya sa cikinta ya juya, sai bayan kusan wata guda ne ta gano cewa lemun ya lalace tun shekara ɗaya da ta wuce. Daga nan ne ta fara zargin ciwon ciki da gudawan da take yi lokaci-lokaci na ad alaƙa da wasu kayan abinci da kayan ƙamshi da Mercy ke kawowa gida.

Ta ce ’yar uwarta ma tana fama da gudawa da gajiya ba tare da wani dalili na zahiri ba, kuma duk lokacin da ta gargaɗe Mercy kan amfani da kayan da suka daina aiki, sai ta kare kanta da cewa, “Da kayan nan suna da illa, da tuni na mutu.”

Tsadar rayuwa ce ta kawo hakan

Masu amfani shafukan sada zumunta da muka nemi daga gare su kan abubuwan da suka fuskanta daga amfani da kayan da suka daina aiki, sun ce sukan duba bayanam wa’adin lalacewar kayan kafin su say, wasu kuma suka ce tsadar rayuwar ke tilasta su sayen kayan da suka tashi aiki.

A’isha Sabitu, wata mai amfani da Facebook, ta ce: “Ina duba bayanin kayan da nake siya sosai. Ni injiniyar abinci ce.”

Amma Seth ya nuna damuwa cewa masu sayar da kayan da suka tashi aiki suna amfani da talaucin jama’a. Ya ce: “Masu sayar da kayan sun san halin da ake ciki, sai su rage farashi kaɗan, jama’a kuma su yi ta rububin saya.”
Amma wasu irin su Alex Mark Ujah, sun ce: “Yanzu komai ya taɓarɓare, abin da muka samu za mu ci.”
An gudanar da wannan bincike ne da tallafin Gidauniyar Daily Trust (DTF) tare da haɗin gwiwar Gidauniyar MacArthur.