✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Layya: Akwai yiwuwar tsananin tsadar raguna

Wannan na zuwa ne bayan da gwamnatin sojin ƙasar Jamhuriyar Nijar taharamta kan fitar da dabbobi zuwa ƙasashen ƙetare

A yayin da Babbar Sallah ke ƙara ƙaratowa, ’yan kasuwar dabbobi sun bayyana fargaba game da yiwuwar farashin ragunan lauya da sauran dabbobi zai yi tashi gwauron a Najeriya.

Wannan na zuwa ne bayan da gwamnatin sojin ƙasar Jamhuriyar Nijar ta sanya takunkumin wucin gadi kan fitar da dabbobi zuwa ƙetare, gami da yawaitar sace-sacen dabbobi a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

A farkon watan nan na Mayu ne Gwamnatin Nijar ta sanar cewa matakin na da nufin daidaita farashi dabbobin layya a cikin gida da kuma tabbatar da wadatarsu ga al’ummarta —waɗanda mafi rinjaye Musulmi ne — kafin zuwan Babbar Sallah a farkon watan Yuni.

Haramcin ya shafi fitar da shanu da tumaki da awaki da raƙuma, tare da alƙawarin tsauraran matakan aiwatar da dokar daga hukumomin tsaro.

Ana fargabar wannan matakin zai yi mummunar illa ga ƙasashe kamar Najeriya da Kwaddibuwa, waɗanda suka dogara da shigo da dabbobi daga Nijar, musamman ma raguna da raƙuma a lokutan da buƙata ta yi yawa.

’Yan kasuwa na neman mafita

’Yan kasuwar dabbobi a manyan kasuwannin Kano da Jigawa na fargabar cewa matakin na gwamnatin Nijar zai iya kawo ƙarancin dabbobin da hauhawar farashi a Najeriya a lokacin Babbar Sallah.

Wani tsohon ɗan kasuwar dabbobi a kasuwar dabbobi ta Wudil a Jihar Kano, Malam Abdullahi Abdul, ya tabbatar da cewa Jamhuriyar Nijar muhimmiyar ƙasa da ke samar da raguna, musamman a lokacin sallar Layya.

Wannan lamari ya sa ’yan kasuwan Najeriya da dama neman hanyoyin samar da dabbobi daga ƙasashe kamar Kamaru da Chadi.

Yayin da ake ƙoƙarin cike giɓin, ’yan kasuwa na tunanin za a samu hauhawar farashi saboda  bambancin canjin kuɗade ƙasar waje.

Alhaji Bello Guri, wani ɗan kasuwar dabbobi, ya buƙaci jama’a da kada su firgita, yana mai cewa sun fara shigowa da dabbobi Najeriya daga wasu ƙasashe.

Ya kuma yi nuni da cewa yadda mutane ke ƙara yawaita kiwon dabbobinsu na Layya zai iya rage dogaro a kan na kasuwa.

Rashin tabbas a Kasuwar Maigatari

Kasuwar Dabbobi ta Duniya ta Maigatari a Jihar Jigawa, wadda muhimmiyar cibiya ce ga kasuwancin dabbobi daga Jamhuriyar Nijar da kuma cikin Najeriya, tana fuskantar koma baya.

Malam Dauda Babandi Gumel ya bayyana kasuwar a matsayin “kufai,” saboda ƙarancin dabbobi, a yayin da ’yan kasuwar Najeriya masu lasisin fataucin dabbobi daga Nijar ke fuskantar rashin aikin yi.

Wannan lamari ya haifar da damuwa game da yiwuwar samun ƙarancin dabbobi gabanin Babbar Sallah ta bana.

Tsadar ta damu masu sayen raguna

Alamomin kasuwa na yanzu sun nuna farashin dabbobi sun tashi sosai idan aka kwatanta da bara.

Ragon da aka sayar N120,000 a shekarar 2024 yanzu farashinsa ya kai tsakanin N170,000 zuwa N200,000. Farashin ɗan maƙi kuma ya ɗaga daga N600,000 zuwa N850,000 zuwa miliyan ɗaya.

Abbas Idris, wani mazaunin Kano, ya nuna damuwarsa cewa mutane kaɗan ne za su iya yin layya a bana idan farashin bai sauka daga yadda yake yanzu ba.

Mutane da yawa, kamar Alhaji Shehu Sharu kuma, sun zaɓi su haɗa kuɗi tare da abokansa su sayi dabbar layya saboda hauhawar farashin.

Malam Idris Isma’ila Zango, wani ma’aikacin gwamnati, ya nuna takaici cewa layya ta fi ƙarfinsa, yana mai cewa raguna sun yi tsada idan aka kwatanta da albashinsa.

Matasalar ta fi haka —Masana

Bayan haramcin da Nijar ta sanar, ƙwararru irin su Dakta Aminu Rimi, masanin kasuwancin dabbobi, sun danganta hauhawar farashin ga wasu dalilai kamar yawaitar sace-sacen dabbobi da kuma gazawar manoma wajen amfani da dabarun kiwo na zamani.

Ya jaddada muhimmancin cikakken aiwatar da Shirin Zamanantar da Kiwo na Ƙasa (NLTP) don inganta samar da dabbobi.

Ibraheem Muazzam, manazarcin harkokin kasuwanci da ke Kano, ya bayyana takunkumin da Jamhuriyar Nijar ta sanya a matsayin mataki da aka yi da lissafi da dabarun siyasa daga gwamnatin sojin Nijar don tabbatar da muhimmancin ƙasar a fannin tattalin arzikin yankin.