Wasu ’yan bindiga sun yi awon gaba da mutane biyar yayin da suka kai hari ana tsaka da cin kasuwa a ƙauyen Dogon Ruwa da ke Ƙaramar Hukumar Wase ta Jihar Filato.
A cewar mazauna, maharan sun wawushe kayayyaki a shaguna inda suka yi awon gaba da kayan abinci da magunguna masu tarin yawa.
- Jami’ar Maryam Abacha ta rufe ɗakunan kwanan ɗalibai a Kano
- Awakin da ke rayuwa sama da shekaru 200 a inda babu ruwa
Aminiya ta ruwaito cewa ’yan bindigar sun kai hari kan kasuwar ce mai tara ɗaruruwan mutane da ke zuwa daga gari-gari makwabtaka domin baza hajoji iri-iri musamman kayan abinci da suka haɗa da shinkafa, fulawa, wake, lemuka da sauransu.
Shafi’i Sambo, wani shugaban matasa a yankin, ya shaida wa Aminiya cewa ’yan bindigar sun kai farmakin da misalin ƙarfe 11 na safe haye a kan babura — inda suka fara harbe-harbe kan mai uwa wabi.
Sai dai ya ce daga bisani jami’an tsaro da suka da sojoji da ’yan sa-kai sun kawo ɗauki tare da bin sawun ɓata-garin da suka kawo farmakin.
Aminiya ta yi ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar Operation Safe Haven, Manjo Samson Zhakom, amma lamarin ya ci tura har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.