Gwamnatin Jihar Sakkwato ta ce ba gazawa ba ce ta sa ta yanke shawarar tattaunawa da ’yan bindigar da suka yanke hukuncin ajiye makamansu ba.
Ta ce wannan hanya ce mafi kyau da za ta kawo zaman lafiya mai ɗorewa a jihar.
- Katolika ta horar da shugabannin al’umma da na addini kan zaman lafiya
- Kotu ta daure mutumin da yake yada bidiyon tsiraici shekara 76 a kurkuku
Wani mai amfani da kafar sada zumunta, Basharu Altine Guyawa, ya soki wannan mataki na gwamnatin.
Amma Mai Bai Wa Gwamnan Jihar Shawara kan Tsaro, Kanal Ahmed Usman (mai ritaya), ya ce manufar gwamnati ita ce ta kawo zaman lafiya, ba don ta kasa ba.
Ya ce, “Mun san kowa na da ‘yancin faɗin albarkacin bakinsa. Amma dole ne mu fayyace dalilin da ya sa Gwamna Ahmed Aliyu ke amfani da hanyoyi daban-daban wajen magance matsalar rashin tsaro, ciki har da tattaunawa da ‘yan bindigar da suka tuba.”
Ya ƙara da cewa abin mamaki ne yadda Guyawa ke sukar wannan yunƙuri.
Ya ce shi ma ya taɓa buƙatar shirin shiga tsakanin gwamnati da ‘yan bindiga domin yin sulhu.
Kanal Usman ya bayyana cewa gwamnati tana amfani da dukkanin matakai biyu; na ƙarfi da na sulhu.
A cewarsa, mutane da yawa a Rabah, Goronyo, Isa, Sabon Birni da wasu yankuna na ta yin hijira.
Manoma sun bar gonakinsu, amfanin gona ya ragu, kuma kasuwanci ya tsaya cak.
Wannan ya jawo ƙarancin abinci da tsadar rayuwa a faɗin jihar.
“Burinmu shi ne mu dawo da zaman lafiya, mu dawo da mutane gidajensu, sannan a sake farfaɗo da harkokin noma da kasuwanci,” in ji shi.
Ya ce har yanzu gwamnati na aike jami’an tsaro inda ya dace.
Amma waɗanda suka tuba da gaske za a karɓe su bisa kulawa da tsari na gyaran hali.
“Wannan ba gajiyawa ba ce ko jin tsoro, wannan dabara ce ta sulhu domin ɗorewar zaman lafiya.”
Amma ya roƙi masu sukar gwamnati da su yi magana cikin hankali.
“Jihar Sakkwato na buƙatar haɗin kai da mafita, ba rabuwar kai da zargi ba. Gwamna Ahmed Aliyu na aiki tuƙuru don kawo zaman lafiya.”