✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ɗan ƙunar baƙin wake ya kashe mutum 10 da bam a Borno

A baya ƙungiyar Boko Haram na amfani da hanyar ƙunar baƙin wake wajen kai hari.

Aƙalla mutum 10 ne suka rasu a daren ranar Juma’a bayan wani ɗan ƙunar baƙin wake ya kai hari da bam a wani wsjen cin abinci da ke garin Konduga, a Jihar Borno.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Borno, ASP Nahum Daso, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce jami’an tsaro da suka haɗa da ‘yan sanda da sojoji na gudanar da bincike domin gano haƙiƙanin abin da ya faru da kuma adadin waɗanda lamarin ya rutsa da su.

Ya ce, “Wani mutum ya kutsa cikin taron mutane da misalin ƙarfe 10 na dare tare da bam, wanda ya tarwatsa kansa kuma ya kashe sama da mutum 10.”

Wani masani kan ta’addanci, Zagazola Makama, ya bayyana cewa mutum 24 ne, suka rasu a sanadin harin, inda ya ce mace ce ta kai harin ƙunar baƙin waken.

Ya ƙara da cewa fashewar ta yi tsanani wanda sai kan matar aka samu.

Bayan harin, an tura tawagar sojoji, ƙwararrun masu binciken bam na ‘yan sanda, ’yan sa-kai, da ƙungiyar CJTF zuwa wajen.

Sun yi bincike amma ba su samu bam na biyu a wajen ba.

An kwashe waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri (UMTH) domin a kula da su.

An kai gawarwakin waɗanda suka rasu zuwa asibitin kuma likitoci sun tabbatar da rasuwarsu.

Makama, ya ce ana ci gaba da tantance sunayen waɗanda abin ya rutsa da su domin a miƙa gawarwakinsu ga iyalansu domin yi musu jana’iza.

Kai harin ƙunar baƙin wake na ɗaya daga cikin dabarun da ƙungiyar Boko Haram ta fara amfani da su a farko-farkon fara ta’addancinta a Najeriya.