Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arziki ta’annati a Nijeriya ta buƙaci Majalisar Tarayyar da ta amince da ƙudirin dokar da zai ba ta damar bincikar ɗaiɗaikun ’yan ƙasar game da yadda suka tara dukiyarsu.
Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya NAN ya ruwaito Shugaban EFCC, Ola Olukayode yana cewa ƙudirin mai suna “Unexplained Wealth Bill” ya je gaban ’yan majalisar tun a majalisa ta tara, wanda suka yi watsi da shi.
- Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 24 a Arewa maso Gabashin Nijeriya
- An kashe mutum ɗaya da ƙona gidaje sama da 100 a Taraba
“Akwai alaƙa mai ƙarfi tsakanin ɓarnar da ake yi arzikin ƙasarmu da kuma matsalar tsaro,” a cewarsa yayin wani taro da kwamatocin majalisar tarayya suka shirya kan arzikin ƙasa.
“Idan kana bincikar ayyukan ’yan fashin daji, da ta’addanci, za ka ga suna da alaƙa da wani nau’i na cin hanci da rashawa, ko kuma karkatar da kuɗaɗen da suka kamata a yi wa al’umma aiki.
“Ina neman ku taimaka min wajen amincewa da ƙudirin “Unexplained Wealth Bill”. Shekara ɗaya kenan ina neman hakan, kuma shi ne dai majalisa ta tara ta yi watsi da shi. “Idan ba mu binciki dukiyar da mutane suka tara ba ba za mu taɓa gyara al’amuran ba.
“Akwai wani da ya yi aiki shekara a wata ma’aikata. Mun lissafa baki ɗayan albashi da alawus ɗinsa. Sai kuma muka gano gidaje biyar da yake da su, biyu a Maitama, uku a Asokoro. Amma kuma ana so mu gabatar wa kotu hujja a kansa kafin mu yi wani bincike. Wannan abin takaici ne.”