Babbbar Kotun Tarayya da ke Kano ta yanke wa fitacciyar ’yar Tiktok, Murja Ibrahim wacce aka fi sani da Murja Kunya hukunicn daurin watanni shida a kurkuku.
Alƙalin kotun Mai Shari’a Simon Amobida ya kuma ba wa Murja zabin biyan tarar Naira dubu 50.
Ya ce saboda yawan mabiyanta a shafinta na Tiktok, an nada ta jakadiyar EFCC da Babban Bankin Najeriya (CBN) wajen wayar da kan mutane kan illar wulakanta Naira a dokar Najeriya.
EFCC ce dai ta maka Murja a kotun, bisa zarginta da wulakanta Naira, bayan bullar wani bidiyo da ta ɗauka tana rawa tana yi wa kanta liƙi da kuɗi a otel ɗin Tahir da ke Kano.
Murja dai ta amsa laifinta, tare da roƙon kotun ta ba ta damar amfani da shafinta mai mabiya fiye da miliyan daya wajen wayar da kan mutane kan illar wulaƙanta Naira, buƙatar da kotun ta amince da ita.