✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tura ’yan China 6 kurkuku kan laifin ta’addanci a Nijeriya

Za a mayar da ’yan China ƙasar da suka fito cikin kwanani bakwai da zarar sun kammala wa’adin gidan yari.

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Jihar Legas ta yi wa wasu ‘yan China shida ɗaurin shekara ɗaya bayan ta same su da laifin ta’addanci da zamba ta intanet.

Sanarwar da hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin Nijeriya ta’annati (EFCC) ta fitar ta ce kotun da ke unguwar Ikoyi ta Jihar Legas ce ta ɗaure mutanen ne bayan ta same su da laifi.

“Masu laifin sun hada da : JIA You (da aka fi sani da A. You) da Wang Zheng Feng ( da aka fi sani da Feng) da Liu San Hua da Chen Wen Yuan da Liu BeiIxingda Wen Zong Xu (da aka fi sani Li Long),” in ji sanarwar.

EFCC ta ce masu laifin suna cikin mutum 792 da ake zargi da hannu a damfara ta hanyar kirifto waɗanda aka kama ranar 19 ga watan Disamba shekarar 2024 a Legas a wani samame da hukumar ta ƙaddamar mai taken “Eagle Flush Operation.”

Bayan an kama su ne aka gurfanar da su a gaban kotu kan zargin aikata ta’addanci da kuma aikata zamba ta intanet.

Sanarwar ta ambato tuhumar da aka yi wa masu laifin na shiga manhajar komfuta da gangan domin lalata tattalin arziki da zamantakewar al’ummar Nijeriya, wanda hakan ya nuna cewa ya aikata laifi da ya saɓa wa dokar hana laifukan intanet ta 2015 da kuma dokar hana ta’addanci ta 2022.

Daga farko dai waɗanda ake zargin sun musanta zargin da aka karanta musu daga takardar tuhumar.

Sai dai kuma a zaman kotun na ranar 23 ga watan Yuni sun sauya matsayarsu zuwa amsa laifi, kuma nan take lauyoyin gwamnati suka nemi kotu ta same su da laifi tare da hukunta su.

“Saboda haka, kotun ta same su da laifi tare da yi wa kowanne daga waɗanda ake tuhumar ɗaurin shekara ɗai-ɗai daga ranar 10 ga watan Disamba na shekarar 2025, da kuma cin kowanne daga cikinsu tarar naira miliyan ɗaya-ɗaya,” in ji sanarwar.

Alƙalin ya kuma ba da umarni ga shugaban hukumar kula da shige da fice ta Nijeriya ya tabbatar cewa an mayar da ’yan China ƙasar da suka fito cikin kwanani bakwai da zarar sun kammala wa’adin gidan yari.

Kazalika, kotun ta ba da umarnin cewa a sallamar da wayoyi da kamfutoci da kuma na’uororin samar da intanet da aka ƙwace daga masu laifin wa Gwamnatin Tarayyar Nijeriya.