Sojoji a Jihar Filato sun ceto wasu mutum 16 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a kan titin Jos zuwa Mangu.
Dakarun Rundunar Operation Safe Haven ne suka ceto mutanen a cikin wata mota da a aka jefar da ita a yankin Mararabar Kantoma da ke Ƙaramar Hukumar Manngu.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, Manjo Samson Zakhom, ya bayyana cewa an ceto mutanen ne da misalin ƙarfe 9 na dare bayan sun tsinci motar a daji babu kowa a ciki.
Ya ce ganin haka ne sojojin rundunar da ke aikin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a jihar suka yi zargin sace fasinjojin cikinta aka yi.
- An yi garkuwa da masu ibada a Kogi
- Yadda kisan mutum fiye da 50 a Filato ya tayar da ƙura
- NAJERIYA A YAU: Dalilan Rikice-Rikice A Jihar Filato
Manjo Samson Zakhom ya ce sojojin suna tsaka da bincike sai ’yan bindigar suka buɗe musu wuta, inda bayan arangamar ɓata-garin suka tsere suka bar matafiyan.
Ya bayyana cewa, a cikin fasinjojin 16 da aka ceto har da ƙananan yara guda shida, kuma duk a ba sau taimakon farko saboda raunukan da suka samu, sannan muka raka su, suka ci gaba tafiyarsu.”