Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa wasu daga cikin sojoji da ’yan siyasa na taimaka wa ƙungiyar Boko Haram ta hanyar ba su bayanai.
A wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na News Central, Zulum ya ce gwamnatinsa za ta ɗauki matakin da ya dace kan duk wanda ke taimaka wa ’yan ta’adda.
- Hajjin 2025: Kashi 79 na maniyyatan Najeriya sun isa Saudiyya – NAHCON
- Gwamnati za ta sayar da gidaje 753 da EFCC ta ƙwato a hannun Emefiele
Ya ce: “Akwai masu bai wa Boko Haram bayanaj a cikin sojoji, ’yan siyasa da sauran jama’a. Za mu ƙarfafa leƙen asiri, kuma mu ɗauki tsattsauran mataki a kansu.”
Gwamna Zulum ya ce dole ne a haɗa kai a yaƙi ta’addanci ta hanyar ƙoƙarin gyara rayuwar al’umma da inganta tattalin arziƙi da samar da ayyukan yi, ba kawai amfani da makamai ba.
Ya bayyana cewa daga cikin sama da mutum 300,000 da suka miƙa wuya daga ƙungiyar Boko Haram, akwai yiwuwar wasu daga cikinsu sun koma daji.
Ya kuma ce rundunar soji ba ta da isassun kayan aiki da za su iya yaƙar ta’addanci yadda ya kamata, inda ya ce ’yan ta’addan na da kayan zamani sama da na sojoji.
Sai dai ya yaba wa sojojin Najeriya saboda irin gudunmawar da suke bayarwa wajen kawo zaman lafiya.
Zulum ya buƙaci Shugaba Bola Tinubu da ya saurari shawarwarin ƙwararru, musamman sojoji, domin magance matsalar tsaro.
“Dole a kafa jami’an tsaron daji cikin gaggawa. Shugaban ƙasa ya saurari mutane masu gaskiya da fahimtar abubuwa. Ka da a ci gaba da siyasantar da matsalar tsaro,” in ji shi.