Sojoji sun yi nasarar cafke wani mutum da ake zargi dan ta’adda ne tare da gano ma’adanar makamai a yayin wani samame da suka yi a Ƙaramar Hukumar Bassa ta Jihar Filato.
Binciken farko ya nuna cewa wanda aka kama ɗin yana da alaƙa da wata ƙungiyar masu aikata laifuka da ke da alhakin kisan wani makiyayi da satar shanu 1,250 a ƙauyen Tomborong, Ƙaramar Hukumar Riyom, a ranar 27 ga watan nan na Mayu.
A safiyar ranar Juma’a, sojoji suka kama wanda ake zargin, bayan samun rahoto game da inda ake zargin ɗan bangar yake ɓoye a ƙauyen Hura.
Yayin wani bincike da aka yi a maboyar wanda ake zargin, jami’an tsaro sun gano bindigar AK-47 guda daya, tare da harsasai 26 na 5.56mm da kuɗi da wasu abubuwan da ake zargin asiri ne.
Wata majiyar soji ta bayyana cewa wanda ake zargin yana tsare a hannun jami’an tsaro kuma yana “bayar da haɗin kai ga masu bincike kan sunaye da wuraren da sauran mambobin ƙungiyar da ma’adanar makamansu suke.”
Sojoji sun tsananta ƙoƙarin gano tare da kama sauran membobin ƙungiyar da ake zargi da alhakin ayyukan laifuka a yankin.