✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 2, sun kama wasu a Kaduna

Rundunar ta yi artabu da 'yan fashin sannan suka kashe biyu daga cikinsu.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, sun kashe ’yan fashi biyu, sannan sun kama wasu biyu a unguwar Makera da ke Kakuri.

Wannan ya biyo bayan musayar wuta da jami’an tsaro suka da ’yan fashin.

Rundunar ta ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 3:10 na dare, bayan da suka samu kiran gaggawa daga mazauna unguwar Gashash a Barnawa.

Rahotanni sun ce ’yan fashi guda takwas sun shiga wani gida ɗauke da bindigu da makamai, sun sace wayoyi, kwamfutoci da sauran kayayyaki.

Bayan kiran gaggawar, DPO na Barnawa, Kakuri da Sabon Tasha tare da sojoji daga Rundunar 312 Artillery Regiment suka bi ’yan fashin har titin Makera.

Kakakin rundunar, DSP Mansir Hassan, ya ce, “Da ’yan fashin suka ga jami’an tsaro, sai suka fara harbi.

“Wannan ya jawo musayar wuta, inda aka kashe biyu daga cikinsu sannan aka kama biyu da ransu.”

Jami’an tsaro sun ƙwato bindiga ƙirar gida, harsasai da wasu makamai.

Sannan sun dawo da kayan da aka sace ciki har da wayoyi bakwai, agoguna uku, kwamfutoci biyu da sauransu.

A lokacin musayar wutar, ɗan sanda ɗaya ya samu rauni amma an miƙa shi asibiti inda yake samun kulawar likitoci.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Rabiu Muhammad, ya jinjina wa jami’ansa kan yadda suka yi aiki cikin gaggawa tare da haɗin kai da sojoji da DSS.

Ya ce rundunar ta ƙudiri aniyar kare jihar daga miyagu.

Ya kuma roƙi al’umma da su riƙa sanya idanu tare da kai rahoton duk wani abun zargi.

Rundunar ta ce tana ci gaba da neman sauran ‘yan fashin da suka tsere.