An harbe wasu mutum biyu da ake zargin ’yan fashi da makami ne a ranar Talata a yayin wani artabu da jami’an tsaro suka yi a unguwar Makera da ke Kakuri a Jihar Kaduna.
Rundunar ta kuma kama wasu mutane biyu da ake zargin tare da ƙwato tarin makamai da kayayyaki masu daraja da aka sace daga mazauna garin.
- An tallafawa iyalan ’yan sanda da Naira miliyan N13.4m a Borno
- Yadda aka kama mai garkuwa da mutane yana tsaka da cin kasuwar shanu a Neja
A cewar kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, lamarin ya fara ne da misalin ƙarfe 3:10 na tsakar dare, inda wasu ’yan bindiga 8 suka kai hari a rukunin gidaje na Estate Gashash da ke Barnawa.
Rahotanni sun bayyana cewa, waɗanda ake zargin ɗauke da bindiga ƙirar gida da kuma wasu muggan makamai, an yi zargin sun yi wa mazauna yankin fashin wayoyin salula da kwamfutar tafi-da-gidanka, da agogunan hannu da na’urorin wasanni da sarƙoƙin masu daraja.
Da aka samu kiran gaggawar, babban jami’in ’yan sanda na Barnawa (DPO), tare da haɗin gwiwar DPO na sashen Kakuri da Sabon Tasha, da kuma jami’an runduna ta 312 na Artillery Regiment Kalapanzi, suka garzaya wurin da lamarin ya faru cikin gaggawa.
Daga baya an bi sawun waɗanda ake zargin har zuwa hanyar Makera, inda aka yi artabu da muggan makamai.
“A fafatawar ne aka kashe biyu daga cikin ’yan fashi da makami, yayin da aka kama wasu biyu,” in ji DSP Hassan.
Ya ce, ana ci gaba da ƙoƙarin kamo sauran ’yan fashin da suka tsere daga yankin.