✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mangu: Gwamnatin Filato ba ta aiko da wakilai don yin ta’aziyya ba — Sarkin Zazzau 

Sarkin ya nuna damuwa kan yadda Gwamnatin Filato ba ta turo wakilai don yi musu ta'aziyya ba.

Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, ya bayyana cewa Gwamnatin Jihar Filato ba ta aiko da wani wakili zuwa Zariya domin yi wa iyalan waɗanda aka kashe a Ƙaramar Hukumar Mangu a Jihar Filato, ta’aziyya ba.

Aminiya ta ruwaito, yadda wasu matasa suka farmaki motar wasu ’yan ɗaurin aure su 31, inda suka kashe 13 daga cikinsu.

Sarkin ya bayyana hakan ne lokacin da jagoran shugabannin addinai, Tsohon Ministan Matasa da Wasanni Solomon Dalung, ya jagoranci wata tawaga zuwa fadarsa domin yin ta’aziyya.

Sarkin ya gode wa tawagar bisa wannan ziyara, amma ya nuna damuwa cewa babu ko ɗaya daga cikin wakilan Gwamnatin Filato da ya zo domin yin ta’aziyya ko duba halin da iyalan mamatan ke ciki.

Ya roƙi Gwamnatin Filato da ta ɗauki matakin gaggawa, kuma a tabbatar da adalci.

Haka kuma, ya jaddada buƙatar haɗin kai a tsakanin al’ummar Arewacin Najeriya bai ɗaya, tare da kiran shugabanni su haɗa kai domin samar da zaman lafiya mai ɗorewa.

Solomon Dalung, ya ce sun zo domin yi wa al’ummar da abin ya shafa da kuma masarautar Zazzau ta’aziyya.

Ya nemi a kwantar da hankali, sannan ya buƙaci gwamnati ta hukunta masu laifin.

Fasto Yohanna Buru, ɗaya daga cikin tawagar, ya bayyana harin a matsayin abin kunya.

Ya kuma ce ya zama dole a cafke masu hannu a harin.

Tawagar ta kuma kai ziyara ga Farfesa Ango Abdullahi kafin su gana da Sarkin Zazzau.

Fasto George T. John, wani daga cikin tawagar, ya ce al’ummar da abin ya shafa na cikin baƙin ciki sosai.

Ya yi Allah-wadai da harin, yana mai cewa hakan mummunan laifi ne.

Yakubu Yusuf, ɗaya daga cikin ’yan uwan waɗanda aka kashe daga Angwan Dantsoho a Ƙaramar Hukumar Kudan, ya gode wa baƙin.

Ya kuma roƙi gwamnatin jihar da ta Tarayya da su taimaka wa marayu da mamatan suka bari.