Wani babban jami’in soja, Laftanar Commodore M. Buba, ya rasa ransa bayan da wani ɓarawon waya ya soka masa wuƙa a ƙirji.
Lamarin ya faru ne a gadar Kawo, lokacin da jami’in ya tsaya domin gyara tayar motarsa da ta fashe yayin da yake kan hanyarsa ta dawowa daga Jaji, inda yake karatu a Makarantar Horas da Sojoji ta Armed Forces Command and Staff College (AFCSC).
- Matawalle ya yi wa Gwamna Lawal da wasu tayin shiga APC
- Gwamnatin Tarayya na shirin farfaɗo da kamfanin ƙarafa na Ajaokuta
Shaidu sun bayyana cewa yayin da jami’in ke cikin gyara tayar, sai wani mutum ya zo ya buƙaci ya ba shi wayarsa.
Jami’in soja ya ƙi bayar da wayar, inda ɓarawon ya ciro suka ya soka masa a ƙirji.
Wani jami’in sa-kai, Suleiman Dahiru, wanda ya ga abin da ya faru, ya yi ƙoƙarin taimaka masa, amma shi ma ɓarawon ya yanke shi da wuƙa a hannu.
Mutanen da ke kusa da wajen take suka kashe ɓarawon da duka.
An garzaya da jami’in sojan zuwa Asibitin Manaal, amma likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.
Daga baya an ɗauki gawarsa zuwa ɗakin ajiye gawarwaki na Asibitin 44 Nigerian Army Reference Hospital da ke Kaduna.
Wani babban jami’in soja da bai so a bayyana sunansa ba, ya ce sojoji da ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro sun shiga cikin gari cikin kaya domin gudanar da bincike da kuma kawar da masu aikata laifuka a Kaduna.
Kakakin rundunar ’yan sandan Kaduna, ASP Mansir Hassan, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana shi a matsayin abin takaici.
Ya kuma tabbatar wa jama’a cewa rundunar ƙoƙarin ƙara tsaurara matakan tsaro a faɗin jihar.