✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun kashe Kwamandan Boko Haram Ibn Khalid a Borno

Sojojin sun kuma ƙwato wasu makamai masu tarin yawa da 'yan ta'addan ke amfani da su.

Dakarun Sojin Operation Hadin Kai, sun daƙile hare-haren Boko Haram a garuruwan Monguno da Bitta da ke Jihar Borno, tare da wani kashe babban Kwamandan ƙungiyar mai suna Ibn Khalid.

Sun kuma kashe ’yan ta’adda da dama, ciki har da wani babban kwamandan ƙungiyar.

Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar, Kapten Reuben Kovangiya, ya ce sojojin sun yi jarumta wajen hana ’yan ta’addan shiga Monguno.

Ya ce sojojin sun yi amfani da manyan makamai wajen mayar da martani, inda suka kashe ‘yan ta’adda da dama, ciki har da wani babban kwamandan Boko Haram mai suna Ibn Khalid.

Yayin da sojojin ke bin sahun ’yan ta’addan da suka tsere, sun ga jini a hanya, alamar cewa wasu daga cikinsu sun jikkata.

Sojojin sun kuma ƙwato makamai da dama daga hannun ’yan ta’addan, ciki har da harsasai, PKT, ma’ajin bindiga AK-47, bam ɗin roka (RPG) da wasu kayayyaki.

Haka kuma, sun samu na’urar ɗaukar bidiyo da ’yan ta’addan ke amfani da ita.

A wasu hare-haren daban da suka gudana a wannan lokaci, sojojin sun kashe ƙarin mayaƙan Boko Haram 17 a dazukan Sambisa, Madagali da Kaga.

Haka kuma sun ƙwato babura da wasu kayan amfani daga hannunsu.

Shugabannin dakarun sun yaba da jarumtar sojojin, kuma sun buƙace su da su ci gaba da yaƙar ’yan ta’addan.