Sojojin Operation SAFE HAVEN da ke aiki a Arewacin Najeriya, sun kama wani mutum da ake zargi da garkuwa da mutane a kan hanyar Wamba zuwa Jos, tare da kuɗi Naira miliyan 13 da kuma makamai.
Wannan kamen ya faru ne a ranar Laraba, 9 ga watan Yuli 2025, a wani shingen bincike da sojoji suka kafa a Agameti, a Ƙaramar Hukumar Sanga ta Jihar Kaduna.
- Muna tunanin sayar da matatun man Najeriya — NNPCL
- Dalilin da ya sa muka gayyaci Sheikh Lawal Triumph – ’Yan sanda
A cewar mai magana da yawun rundunar, Manjo Samson Zhakom, sojojin sun dakatar da wata mota ƙirar Volkswagen mai lamba JJN 336 YZ, ɗauke da mutane uku.
Amma biyu daga cikin su sun tsere kafin a fara bincike.
Bayan duba motar, sojojin sun gano bindigogi biyu ƙirar AK-47, harsashi da yawa, da kuma jini a cikin motar.
Wanda aka kama ya yi ƙoƙarin bai wa sojoji cin hancin kuɗi domin su sake shi, amma suka ƙi amincewa.
Sojojin na ci gaba da ƙoƙarin kamo waɗanda suka tsere domin tabbatar da doka da oda a yankin.