✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muna tunanin sayar da matatun man Najeriya — NNPCL

Shugaban ya ce an shafe shekaru ana gyaran matatun amma ba sa aiki yadda ya kamata.

Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL), ya ce ya fara tunanin yiwuwar sayar da matatun man ƙasar nan.

Shugaban kamfanin, Bayo Ojulari ne, ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da Bloomberg.

Ya ce yanzu haka kamfanin yana sake duba yadda ake gudanar da matatun, kuma ana sa ran kammala wannan nazari kafin ƙarshen shekara.

Da yake magana a taron OPEC karo na tara da aka yi a Birnin Vienna, na ƙasar Austria, Ojulari ya ce gyaran tsofaffin matatun gwamnati ya wuce yadda ake tsammani.

Najeriya na da matatu huɗu; Fatakwal, Warri da Kaduna, amma sun daɗe suna fama da matsaloli kuma ba sa aiki yadda ya kamata.

An daɗe ana kiranye-kiranyen bayar da su ga kamfanonin masu zaman kansu domin kula da su yadda ya kamata.

A watan Nuwamban 2024, NNPCL ta sanar da cewa matatar Fatakwal ta fara tace mai, amma daga bisani aka rufe ta a watan Mayun 2025 saboda matsalolin da suka shafi gyara.

Sauran matatun na Warri da Kaduna har yanzu ana kan gyaran su.

Ojulari ya ce, “Mun kashe kuɗi da yawa kuma mun kawo sabbin dabaru, amma wasu daga cikinsu ba su yi aiki yadda ya kamata.

“Waɗannan matatun tsofaffi ne, kuma suna da wahalar gyaruwa.”

Ya ce yanzu NNPCL na gudanar da cikakken bincike kan tsarin gyaran matatun, kuma sakamakon wannan bincike na iya haifar da sauye-sauye, ciki har da yiwuwar sayar da su.

“Muna fatan kammala binciken nan kafin ƙarshen shekara,” inji shi.

“Sayar da matatun na cikin zaɓin da muke dubawa. Za mu yanke shawara ne bayan mun ga sakamakon wannan bincike.”