✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba lallai matatun man gwamnati su sake aiki ba har abada a Najeriya – Ɗangote

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Ɗangote, ya ce yana da shakku a kan ko matatun mai mallakin gwamnatin Najeriya za su ƙara aiki a…

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Ɗangote, ya ce yana da shakku a kan ko matatun mai mallakin gwamnatin Najeriya za su ƙara aiki a nan gaba.

Najeriya dai na da matatun mai guda hudu mallakinta a biranen Fatakwal da Warri da Kaduna.

Amma attajirin ya ce matatun man waɗanda ke ƙarƙashin kulawar Kamfanin Mai na Najeriya (NNPCL), sun laƙume sama da Dalar Amurka biliyan 18 wajen gyaransu, amma har yanzu sun ƙi aiki.

Ɗangote ya bayyana hakan ne ranar Alhamis lokacin da ya karɓi baƙuncin mambobin shugabannin kamfanoni wadanda ke Karatu a Lagos Business School, a rangadinsu a matatar Dangote da ke Legas.

‎Ya ce matatar man shi mai ƙarfin tace ganga 650,000 a kullum yanzu kusan kaso 50 na aikinta a kan tace man fetur ne, yana mai cewa hatta matatun man gwamnati kaso 22 na karfinsu suke sakawa a harkar tace man fetur ɗin.

A cewar attajirin na Afirka, “Mun taɓa sayen matatun man Najeriya daga hannun tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo a watan Janairun 2007.

“Amma lokacin da marigayi Shugaban Kasa Umaru Yar’aduwa ya zo, tsofaffin manajojin matatun sai suka ce masa an sayar da matatun a ƙasa da ainihin ƙimar su a kasuwa, Obasanjo ya ba mu kamar kyauta ne kawai lokacin da zai tafi. Dole sai da muka mayar da su saboda an samu canjin gwamnati.

‎“A lokacin, manajojin matatun sun shaida wa Yar’aduwa cewa matsayin za su tashi, kawai ƙanin kyauta Obasanjo ya ba mu lokacin da zai tafi.

“Yanzu haka maganar da ake yi, an kashe sama da Dala biliyan 18 wajen gyaran su, amma har yanzu ba sa aiki. Kuma ba na tunani, ina da kokwanto a kan yiwuwar sake aikinsu a nan gaba,” in ji shi.

‎Dnagote ya kwatanta ƙoƙarin da ake yi na gyara matatun da na mutumin da ke kokarin zamanantar da motar da ya saya sama da shekaru 40 da suka wuce ne, alhalin zamani ya riga ya wuce wajen.