✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dangote: Har yanzu gidajen mai ba su rage farashin mai ba

Daga ranar 16 ga Afrilu, 2025, farashin man fetur zai tashi daga N865 zuwa N835.

A karo na biyu a cikin mako guda, matatar mai ta Dangote ta sanar da rage farashin man fetur.

Daga ranar 16 ga Afrilu, 2025, farashin man fetur zai tashi daga N865 zuwa N835.

Wannan dai shi ne karo na biyu da aka rage farashin a cikin mako guda yayin da matatar man Dangote a baya ta rage farashin daga N880 zuwa N865 kan kowacce lita.

Sai dai kuma, har ya zuwa ranar Laraba, farashin bai canja ba a galibin gidajen mai da suka haɗa da cibiyoyin sayar da man fetur na Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPCL).

Yayin da ’yan kasuwa ke maraba da matakin da Dangote ya ɗauka na ragin, duk da haka sun bayyana ra’ayoyinsu daban-daban kan abin da suka kira, “raguwa ba bisa ƙa’ida ba” wanda ke nuna asarar a harkar kasuwancin.

Babban jami’in hulɗa da jama’a na kamfanonin Dangote, Anthony Chiejina, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce, “Yanzu za a riƙa samun man fetur na Dangote a farashi kamar haka a duk gidajen sayar da man da suke da haɗin gwiwa da mu….”

Ya ce, manyan abokan hulɗa da suka haɗa da: MRS, AP (Ardova), Heyden, Optima Energy, Hyde da Techno Oil, za su riƙa ba da man fetur a kan Naira 890 kowace lita, ƙasa da N920 a Legas.

A Kudu maso Yamma farashin zai kasance N900 kowace lita, an rage shi daga N930 yayin da a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya farashin zai zama N910 kowace lita, an rage shi daga N940.

A Kudu maso Gabas, Kudu maso Kudu, da Arewa maso Gabas, farashin zai kasance N920 kowace lita, ƙasa da N950.