✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dangote ya sake rage farashin man fetur

Matatar mai ta Dangote ya sanar da sake sabon ragin farashin man fetur na N15 a gidajen da ke hulɗa da shi.

Kamfanin Dangote wanda ya mallaki matatar mai ta Dangote ya sanar da sake sabon ragin farashin man fetur na N15 a gidajen da ke hulɗa da shi.

A wata sanarwa da kamfanin ya fitar a ranar Alhamis, ya ce a sakamakon wannan ragi, ‘yan Najeriya za su sayi man fetur a kan farashi kamar haka: Naira 875 kowace lita a Legas; Za a sayar Naira 885 kowace lita a yankin Kudu maso Yamma; A Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya za a sayar kan Naira 895 kowace lita; yayin da za a sayar da shi kan Naira 905 kan kowace lita a Kudu maso Gabas, Kudu maso Kudu, da Arewa maso Gabas.

Waɗannan farashin za su yi aiki ne ta duk abokan hulɗa.

A cewar matatar, abokan huldar sun haɗa da gidajen man kamfanonin: MRS, AP, Heyden, Optima, TechnOil, da Hyde.

Matatar ta yi kira ga sauran ‘yan kasuwa da su haɗa kai da abokan hulɗarta, ta yadda za su nuna goyon bayansu ga manufofin farko na Shugaba Bola Tinubu, da ke ba da shawarar ba da fifiko ga kayayyaki da ayyuka da ake samarwa a cikin gida.

Tun lokacin da ta fara aiki, matatar man Dangote ta ci gaba da aiwatar da dabarun rage tsadar kayayyaki da nufin sauƙaƙawa ’yan Najeriya.

A watan Fabrairun 2025, kamfanin ya yi ragin farashin man fetur sau biyu, wanda ya haifar da raguwar jimillar Naira 125 kan kowace lita.

Hakan ya biyo bayan ragin kusan Naira 45 a kowace lita a watan Afrilu.

Sabon farashin man fetur na Matatar Mai ta Dangote