Jami’an gwamnati daga jihohin Gombe da Bauchi sun gudanar da wani taron kwana biyu tare da wakilan kamfanin NNPC da Kamfanin AOML, waɗanda ke gudanar da aikin hakar danyen mai a yankin Kolmani.
An kira taron ne don neman ƙarin bayani kan matakan da AOML ta riga ta ɗauka da kuma gyara kura-kuran da aka gani daidai da Dokar Masana’antar Man Fetur (PIA), da nufin kauce wasau matsalolin da suka addabi sauran yankuna masu arzikin mai.
Wata sanarwa da Kwamishinan Ma’adinai da Makamashi na Jihar Gombe, Sanusi Ahmed Pindiga, ya fitar, ta ce Kwamitin Haɗin Gwiwa da ke wakiltar jihohin biyu ya gano muhimman fannoni huɗu da ke kawo damuwa, waɗanda suka haɗa da sayen filaye, rashin gudanar da ‘Yancin Aiki (FTO), rashin bin ka’idojin Alhakin Ci Gaban Al’umma (CSR) daga AOML, da kuma gibin sadarwa.
Ya ƙara da cewa don magance matsalolin da aka gano, Kwamitin Haɗin Gwiwa ya yanke shawarar cewa za a kammala sayen filaye da zarar AOML ta samar da takardun biyan kuɗi da suka dace, yayin da NNPC zai ta bi diddigin kamfanin kan biyan kuɗin FTO don hakar mai.
- Jami’an Sibil Difens sun bude wuta a garin Jos
- Za mu gina mayankar dabbobi ta Naira biliyan 3 a Gombe —Gwamnati
A cewarsa, za a gudanar da cikakken binciken buƙatu a cikin al’ummomin masu makwabtaka da rijiyar man da waɗanda suka fuskanci matsaloli a sakamakon aikin hakar man don jagorantar shirye-shiryen ayyukan Alhakin Ci Gaban Al’umma (CSR).
Bugu da kari, za a kafa tsarin sadarwa don tabbatar da ingantacciyar mu’amala tsakanin masu gudanar da aikin Filin Mai na Kolmani da dukkan masu ruwa da tsaki.
“Mahalarta taron sun nuna godiya ga shiga tsakani a kan lokaci kuma sun sake jaddada jajircewarsu ta haɗin gwiwa don tabbatar da cewa aikin Filin Mai na Kolmani ya ci gaba ta hanyar da za ta amfani dukkan masu ruwa da tsaki kuma ta bi doka,” in ji Pindiga.
Ya ƙara da cewa: “Sun kuma sake jaddada fatansu cewa burin samun mai da iskar gas na Arewacin ƙasar da aka daɗe ana jira zai tabbata, kuma zai kawo ci gaban tattalin arziki ga yankin.”