Jami’an tsaro sun hana gudanar da taron Kwamitin Amintattu na Jam’iyyar adawa ta PDP da aka shirya a hedikwatar jam’iyyar.
A safiyar Litinin din nan ne jami’ai da yawa ne suka kutsa cikin zauren da aka tsara gudanar da taron inda suka bukaci wadanda suka hallara da su watse.
Jami’an tsaro da aka jibge a hedikwatar babbar jam’iyyar adawar sun hana mambobin kwamitin amintattu gudanar da taronsu a hedikwatar jam’iyyar.
Har zuwa lokacin hada da wannan rahoto, wasu daga cikin ’yan kwamitin amintattun na PDP suna tattaunawa a kan halin da ake ciki.
Mun samu rahotannin cewa jami’an sun umurci mambohin su bar ofishin jam’iyar domin ganin ba a gudanar da wani taro a ofishin jam’iyar ba.