Jagoran sabuwar jam’iyyar ADC, Ralph Nwosu, ya bayyana cewa tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, zai jagorance su wajen karɓar mulki daga hannun Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.
Jam’iyyar haɗakar, wacce ta ƙunshi fitattun ’yan siyasa, ta naɗa David Mark a matsayin Shugaba, tare da tsohon Gwamnan Jihar Osun, Rauf Aregbesola, a matsayin Sakatare.
- ’Yan sanda sun kama wani mutum da jabun kuɗi a Gombe
- Ambaliya: Zulum ya bada umarnin tallafa wa mutanen Damboa da Askira-Uba
A wajen babban taron da ta gudanar a cibiyar Yar’Adua da ke Abuja, Nwosu ya ce: “Mun sauka daga muƙamanmu domin mu bai wa David Mark dama ya jagoranci wannan tafiya zuwa fadar shugaban ƙasa.”
Ya yaba wa Aregbesola, wanda ya taɓa kasancewa abokin siyasar Tinubu, inda ya ce mutum ne mai aiki tuƙuru da kishin ƙasa.
Nwosu ya ƙara da cewa: “’Yan Najeriya sun gaji. Sun ƙosa da sauyi. Wannan haɗaka da muke yi na da matuƙar muhimmanci.
“Ina goyon bayansa sosai, kuma ba zan huta ba har sai mun isa fadar shugaban ƙasa, mun rera taken ƙasa a can. Najeriya na cikin tsaka mai wuya.
“Rayuka na salwanta kullum. Shugabanninmu na gaba su fitar da Najeriya daga wannan halin, su kai ta ga ci gaba. Za mu iya!”
Ya kuma gargaɗi masu sukar wannan haɗakar da cewa ba ’yan jam’iyyar ADC ba ne.
“Babu buƙatar yin nadama a kan abin da muka yi yau. Wannan tafiya ce mai wahala, dole mu kasance a shirye.”
Daga cikin fitattun mutane da suka halarci taron har da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar; ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi.
Sauran sun haɗa da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai; tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi; da tsohon Gwamnan Jihar Imo, Emeka Ihedioha, da sauransu.