Daga ƙarshe dai Shugaban Kasa Bola Tinubu ya sa hannu kan sababbin dokokin haraji guda hudu da a baya suka jawo cece-kuce da zazzafar muhawara a faɗin Najeriya.
An dai sanya hannun ne a fadar shugaban kasa ta Aso Rock da ke Abuja ranar Alhamis, inda shugaban ya ce dokokin za su bunkasa harkokin hada-hadar kudade da tattara haraji a kasar.
- NAJERIYA A YAU: Ko Wadanne Dalilai Ne Ke Hana Mata A Arewa Koyon Ilimin Kimiyya?
- Sheikh Dahiru Bauchi ya cika shekara 101 a duniya
A kwanan nan ne dai Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta amince da kudurorin su zama doka bayan tafka zazzafar muhawara a zaurukan majalisun guda biyu.
Daga cikin waɗanda suka halarci bikin saka hannun akwai Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da Kakakin Majalisar Wakilai, Tajuddeen Abbas da shugabannin masu rinjaye na majalisun biyu da kuma shugabannin kwamitocin kudi na majalisun.
A ranar Laraba ce dai mai magana da yawun shugaba Tinubu, Bayo Onanuga, ya sanar da cewa da zarar sun fara aiki, kudurorin za su bunkasa hanyoyin tattara kudaden shiga a kasar.
A cewarsa, ana sa ran dokokin za su kuma karan yawan kudaden harajin da Najeriya ke samu sannan sau bunkasa harkokin kasuwanci su kuma haɓaka harkokin zuba jari daga ’yan kasuwar gida da na ƙetare.
Sai dai Hukumar Tattara Haraji ta Kasa (FIRS) ta ce dokokin ba za su fara aiki ba sai a watan Janairun 2026.
A baya dai saɗarorin dokokin da suka fi yamutsa hazo su ne na batun rarraba harajin kuɗaɗen sayen kaya na VAT da yadda za a raba shi.
Sai dai majalisar dattawa da ta wakilai ta gyara saɗarorin kafin ta amince da su tare da samun amincewar akasarin ’yan majalisar.